Yadda Ake Rice Bread Cikin Sauki

0
62

Idan za’a yi biredin ana buƙatar a niƙa fulawar tayi laushi sannan a haɗa da fulawar alkama domin a sami good end product mai kyau, tayaya zamu sami good end products zamu iya 50

50 na alkama da kuma shinkafa ko kuma zamuyi 70% alkama da kuma 30% shinkafa domin kamar yadda muka faɗa a baya itama shikafa bata da sinadarin protien wanda yake fitar da (Gliadin da kuma Gluten) in da su wannan sinadaren ke bawa fulawa danƙo idan ana sarrafata. Idan muka ce zamuyi breadin fulawar shinkafa zalla tun daga murji bazamu sami abunda mukeso ba sai bincike ya nuna cewa proportion of 70 : 30 wheat rice is the best when it’s comes to bread making in da shi breadi na neman wannan danƙo domin ya tashi kuma yayi laushi sannan bazai  farfashe ba idan an gama gasa bread ɗin.

Haɗa  fulawar alkama ya tasar da wannan biredi daga gluten – free bread idan za’a iya yi na shinkafa 100% fulawa.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.

Idan zamuyi biredi mai kyau na shinkafa da farko muna buƙatar shinkafa mai kyau da kuma tsafta.

ABUBUWAN DA AKE BUƘATA 
  1. fulawar shinkafa   30g
  2. fulawar alkama (normal wheat fulawa) 70g
  3. ruwan ɗomi
  4. milk (madara)
  5. yeast
  6. butter 1 tablespoon cokali ɗaya babba.
YADDA AKE HAƊAWA
  1. A haɗa yeast da ruwan madara mai ɗumi a ajiye a gefe.
  2. A zuba fulawar shinkafar data alkama acikin kwano mai zurfi sai a zuba bota cokali ɗaya a chakuɗa da ɗan gishiri da siga.
  3. sai a kawo ruwan yeast da madara a haɗa a kwaɓa.
  4. A shafawa roba mai kyau mai a sami  roba a mulmula a saka aciki. A rufe da tsumma mai kyau a rufe ya kai wuri mai ɗumi ko kuma akai rana a barshi ya tashi kamar na minti 50 zuwa awa ɗaya.
  5. Idan ya tashi sai a barbaɗa a tebur ɗin kichin (tebur ɗin aiki) sannan a sake murza fulawar na minti 3 – 4 a yanka yadda ake son girman
  6. A sami abun gashin biredi mai kyau a shafa bota sannan a barbaɗa fulawar a ciki. A ɗauko fulawar a saka aciki a rufe abarshi ya sake tashi na minti 30 kafin a saka acikin oven a gasa.
Doughnut:- 13
  1. Da wannan kwaɓin zamu iya yin doughnut ɗinmu sai dai shi donut zamu murza a yanka da roba mai round sannan a saka robar lemo a cire tsakiya idan kuma akwai abun yankan donut sai a fidda shape ɗin da shi.
  2. A soya har sai yayi golden brown

Domin karanta Abinda Ya Kamata A Sani Game Da Kabeji (Cabbage) Danna nan 

labarin da ya wuceYadda Ake Rice Crepe Cikin Sauki
Labarin na GabaYadda ake Rice Biscuits (COCONUT)
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.