Tag: Cikin Sauki

  • Yadda Ake  Rice Cocktail Bites Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauƙi

    Abubuwan da ake buƙata domin haɗa Rice Cocktail Bites Cikin Sauƙi su ne:

    1. Rice fulawa 2 cups
    2. Garin wake 1 cup
    3. curry powder  ½ teaspoon 
    4. Baking powder 1 ½ teaspoon
    5. Barkono dakakke idan akwai yaji a saka dai dai yadda akeso.
    6. sinadarin ɗanɗano dunƙule 2
    7. Tafarnuwa garin  1 teaspoon
    8. bota ko mai cokali uku.
    9. mai na suya.
    Yadda Ake Haɗawa
    1. A haɗa komai cikin roba mai kyau sai a zuba ruwan ɗumi a kwaɓa ya yi kauri
    2. A samu extnuder ko injin taliya a fitar da shape a soya acikin mai me zafi.
    Domin sanin yadda ake miyar karkashi da kuɓewa danna nan
  • Yadda Ake Ricei Threads Cikin Sauki

    Yadda Ake Ricei Threads Cikin Sauki

    Abubuwan Da’ake Da Buƙata

    1. Rice fulawa   2 cups
    2. siga     ¼ cup
    3. Salt   pincb
    4. egg   1
    5. cinnamon   1 tablespoon
    6. Baking powder   1 teaspoon
    7. butter    2 tablespoon
    8. vegetable oil na suya.
    Yadda Ake Haɗawa
    Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan
    1. A ɗibi kofi ɗaya na fulawar a haɗa siga, gishiri, kirfa, Baking powder da bota a juya a ajiye a gefe guda.
    2. cikin ‘yar tukunya a zuba ruwa kamar ¼ kofi a ɗora a wuta sannan a zuba ragowar fulawar a juya kamar tuƙin tuwo na minti ɗaya sai a sauke.
    3. Idan an sauke a ɗauko haɗin fulawar a zuba cikin tuwon fulawar a kwaɓa ya kwaɓu da kyau sai a fasa ƙwai a sake murzawa
    4. Idan akwai extruder a saka a babban lamba ana soyawa acikin mai me zafi har sai ya soyu.
    5. Idan babu za’a sami abun murjin taliya (injin murza taliya) a murza ana saka fulawar don karta haɗe. Idan mai ya yi zafi sai a soya.

    Domin karanta Yadda ake Rice Biscuits (COCONUT) Danna nan

  • Yadda Ake Rice Bread Cikin Sauki

    Yadda Ake Rice Bread Cikin Sauki

    Idan za’a yi biredin ana buƙatar a niƙa fulawar tayi laushi sannan a haɗa da fulawar alkama domin a sami good end product mai kyau, tayaya zamu sami good end products zamu iya 50

    50 na alkama da kuma shinkafa ko kuma zamuyi 70% alkama da kuma 30% shinkafa domin kamar yadda muka faɗa a baya itama shikafa bata da sinadarin protien wanda yake fitar da (Gliadin da kuma Gluten) in da su wannan sinadaren ke bawa fulawa danƙo idan ana sarrafata. Idan muka ce zamuyi breadin fulawar shinkafa zalla tun daga murji bazamu sami abunda mukeso ba sai bincike ya nuna cewa proportion of 70 : 30 wheat rice is the best when it’s comes to bread making in da shi breadi na neman wannan danƙo domin ya tashi kuma yayi laushi sannan bazai  farfashe ba idan an gama gasa bread ɗin.

    Haɗa  fulawar alkama ya tasar da wannan biredi daga gluten – free bread idan za’a iya yi na shinkafa 100% fulawa.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.

    Idan zamuyi biredi mai kyau na shinkafa da farko muna buƙatar shinkafa mai kyau da kuma tsafta.

    ABUBUWAN DA AKE BUƘATA 
    1. fulawar shinkafa   30g
    2. fulawar alkama (normal wheat fulawa) 70g
    3. ruwan ɗomi
    4. milk (madara)
    5. yeast
    6. butter 1 tablespoon cokali ɗaya babba.
    YADDA AKE HAƊAWA
    1. A haɗa yeast da ruwan madara mai ɗumi a ajiye a gefe.
    2. A zuba fulawar shinkafar data alkama acikin kwano mai zurfi sai a zuba bota cokali ɗaya a chakuɗa da ɗan gishiri da siga.
    3. sai a kawo ruwan yeast da madara a haɗa a kwaɓa.
    4. A shafawa roba mai kyau mai a sami  roba a mulmula a saka aciki. A rufe da tsumma mai kyau a rufe ya kai wuri mai ɗumi ko kuma akai rana a barshi ya tashi kamar na minti 50 zuwa awa ɗaya.
    5. Idan ya tashi sai a barbaɗa a tebur ɗin kichin (tebur ɗin aiki) sannan a sake murza fulawar na minti 3 – 4 a yanka yadda ake son girman
    6. A sami abun gashin biredi mai kyau a shafa bota sannan a barbaɗa fulawar a ciki. A ɗauko fulawar a saka aciki a rufe abarshi ya sake tashi na minti 30 kafin a saka acikin oven a gasa.
    Doughnut:- 13
    1. Da wannan kwaɓin zamu iya yin doughnut ɗinmu sai dai shi donut zamu murza a yanka da roba mai round sannan a saka robar lemo a cire tsakiya idan kuma akwai abun yankan donut sai a fidda shape ɗin da shi.
    2. A soya har sai yayi golden brown

    Domin karanta Abinda Ya Kamata A Sani Game Da Kabeji (Cabbage) Danna nan 

  • Yadda Ake Rice Crepe Cikin Sauki

    Yadda Ake Rice Crepe Cikin Sauki

    Abubuwan da ake bukata domin haka rice crepe cikin sauki batare da bata lokaci ba

    1. Rice fulawa   1 cup 
    2. Salt  pincb
    3. non – fat milk (sachet 1)
    4. Baking powder   ½ teaspoon
    5. warm water  ½ cup
    6. ƙwai manya guda biyu.
    Yadda Ake Haɗawa

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.

    1. kwaɓa dukkan ingredient ɗin a cikin roba mai zurfi idan kwaɓi yayi kauri ana iya ƙara ruwa ya ɗanyi ruwa-ruwa kamar kwaɓin wainar fulawa.
    2. A saman tandar suya mai zafi a shafa mai da ɗan tissue sannan a zuba a barshi ya soyu ko kuma in anga ya fara bubbles sai a juya ɗayan ɓarin.
    3. za’a iya ci da miya ko peppered soup ko da zuma as breakfast.
    4. za’a iya ci da yankakkiyar ayaba da nutella ko strowberry ko kuma a saka haɗin su cabbage, nama, mayonnoise da cheese.

    Domin karanta Yadda Ake Rice Cake Danna nan 

  • Yadda Ake Pancake Cikin Sauki

    Yadda Ake Pancake Cikin Sauki

    Pancake abinci mai sauƙin sarrafawa kuma na karin kummalo ko kuma domin yara ‘yan makaranta ana iya cin pancake da lemo ko madara ko shayi.

    ABUBUWAN BUƘATA
    1. fulawar shinkafa 1 ½  kofi ɗaya da rabi
    2. Madarar ruwa rabin kofi 1 ½ cup
    3. kwai 2
    4. Baking powder (baƙin hoda) ½ teaspoon
    5. sugar ½ kofi
    6. flavour (vanilla flavour) 1 teaspoon.
    7. Bota (butter) ¼ cup
    8. Dafaffiyar shinkafa kofi ɗaya 1 cup.
    Yadda Ake Haɗawa

    Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Abinci A Lafiyance? danna nan.

    1. A haɗa dry ingridients cikin roba mai tsafta (fulawa, baƙin hoda).
    2. A cikin wata roba mai zurfi a sa bota da siga ayita juyawa har sai yayi fari.
    3. A fasa kwai a zuba ana juyawa.
    4. Bayan nan sai a zuba madara, filabo a juya.
    5. A ɗauko fulawa mai baƙin hoda a zuba a juya da kyau sannan a zuba dahon shinkafa.
    6. A sami abun gashi mara kamu (non- sticky frying pan) A shafa mai sai a zuba gasarar pancake idan ya gasu sai a juya ɗayan ɓarin shima ya gasu.
    7. Haka za’a yi tayi har a gama da gasarar.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.