Abinci na nufin duk wani abu da za a iya ci ko sha, ba tare da ya yi illa ba a jikin ɗan Adam, wanda ke haifar da ƙarfi, lafiya, kuzari, gina jiki da ƙara ƙarfin ƙasusuwa, dama wasu abubuwan da dama.
Za mu iya cewa abinci shi ne jigon rayuwar ɗan Adam, wanda ɗan Adam ba zai iya rayuwa ba tare da shi ba.
Misalan abinci sun haɗar da shinkafa, doya, makani, alkama, dankali, gero, dawa, lemo, ayaba, kabeji, da dai sauransu.
Kamar yadda muka san abinci nau’ika daban-daban ne, haka ma amfaninsu yake daban-daban.
Wani abincin na ɗauke da sinadaran dake ƙara wa jiki kuzari, wani ƙarfi, wasu ƙarfin ƙasusuwa dama wasu amfaninnikan da dama.
Yana da kyau a ilmin kiwon lafiyar ɗan Adam a kowacce rana ya kasance ya ci dukkanin nau’ikan abincin da za su gina jiki,
Kuma su ba wa kowane ɓangare na jikin mutum, abinda yake buƙata wanda a Turance ake kiran sa da BALANCE DIET
Amfanin abinci a jikin ɗan Adam yana yawa, kuma muna samun dukkanin ƙarfinmu ne da kuzari daga jikin abincin wanda ake kiransa da NUTRITION.
Gaba ɗaya abinci da muke ci a rayuwarmu, wanda ke ba mu lafiya da kuzari wanda a Turance ake kiran sa da DIET.
Abinci a iya kuzari yake da lafiya yake ƙara wa ɗan Adam, ba har kariya daga cututtuka da dama
misali: cin shinkafa na taimaka mutum wajen rage cikon gabobi, rage yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya dama abubuwa da dama.
Kamar yadda abinci ya kasu kashi-kashi, haka ma ya karkasu a kan mutane wato NUTRITION wanda muke samu a jikin abinci. Misali yara, mai ciki, mai shayarwa, marasa lafiya da ma tsofaffi.