Mene Ne Ma’anar Diet?

0
1436

DIET :

Na nufin abincin da ɗan Adam ke ci ko sha a kullum, wanda ya haɗar da komai da komai da yake ba wa ɗan Adam kuzari da kuma ƙarfi.

Cin abinci mai lafiya na ɗaya daga cikin manyan dalilan dake samarwa ɗan Adam lafiya. Jikin mutum a kullum akwai sinadarai masu mahimmanci da kariya, da yake buƙata wanda suke inganta lafiya da garkuwar jiki.

Misalan sinadaran dake ƙara ƙarfin ƙashi wato CALCIUM daban da waɗanda suke gina garkuwar jiki wato BODY BUILDING FOOD a Turance. A kowacce rana jikin mutum na buƙatar dukkanin abin da zai inganta lafiyarsa.

Cin abinci lafiyayye da shan tsabtataccen ruwa na cikin abin da yake ƙara wa mutum lafiya da ƙarfi a jiki.

Domin sanin mene ne abinci a lafiyance danna koren ruutun nan

labarin da ya wuceMene Ne Abinci A Lafiyance?
Labarin na GabaWace Ce Ta Karɓi Haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)?
Khadija Yusha'u (Amira)
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.