Yadda Ake Irish Pizza

0
616

A yau za mu koyi yadda ake irish pizza, wato pizzar danakin Turawa.

Tana da matuƙar daɗi da sauƙin sarrafawa, Ana iya cin ta a karin kumallo ko a abincin dare

Abubuwan da ake buƙata: 

Irish
Ƙwai
Albasa
Taruhu
Tattasai ja da kore
Koren wake
Sweet corn
Karas
Maggi da sauran spices

Yadda ake haɗawa 

Ki fere irish ɗinki, ki yi masa yankan cubes, sai ki soya sama-sama da ɗan gishiri kaɗan, ki ajiye a gefe.

Ki wanke kayan miyarki da aka lissafo a sama, sai ki yanka su su ma, a soya sama-sama da ɗan mai, kaɗan, sai a saka maggi da spices ɗin da kike buƙata. Sai ki ɗauko wannan Irish din da kika soya, ki zuba cikin kayan miyar da kika soya, ki haɗa su guri ɗaya, ki gauraye su, su haɗe, sai ki fasa kwai, ki zuba a kai, sai kisa a tray ki sa cikin oven, kar wuta ta yi yawa, da kin ji ya fara ƙamshi, sai ki fitar ki yi masa yankan pizza.

Domin sanin yadda ake danbun nama danna nan

labarin da ya wuceShekarar Annabi Muhammad(S.A.W) Nawa Mahaifinsa Ya Rasu?
Labarin na GabaYadda Ake Potato Cake.