Yadda Ake Potato Cake.

0
1061

A yau za mu koyi yadda ake Potato cake, ana kiran shi da cake decorating  dankali a Hausance, wanda ya kasance abinci mafi daɗi da gamsarwa, ga sauƙi wurin haɗin. Ku biyo ni don jin yadda za mu yi wannan abincin.

Abubuwan da ake buƙata,

 • Dankalin Turawa
  Maggi
  Flour
  Niƙaƙƙen nama
  Attaruhu da albasa
  Kwai da butter

YADDA AKE HAƊAWA:

Da farko za ki fere dankali, sai ki dafa shi, sai ki sami nama niƙaƙƙe, ki silala da kayan ƙamshi, sai sauke, ki samu bowl ki zuba dankalin, ki marmasa shi, sai ki jajjaga attaruhu da albasa da Maggi, sai ki haɗa a cikin wannan dankalin, sai ki fasa ƙwai, ki barbaɗa flour kaɗan, kamar yanayin dai kaurin cake, sai ki sa butter cokali biyu, sai ki dauko gwangwanin cake, ki shafa butter, ki sa a baking tray ki gasa. A ci daɗi lafiya.

Domin sanin yadda ake irish pizza danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Irish Pizza
Labarin na GabaYadda Ake Haɗin Kayan Ƙamshi