Yadda Ake Ice Cream Custard

0
447

Ice cream custard ya kasance abin sha mai daɗi, mai sauƙin sarrafawa, ba tare da shan wahala ba, mafi yawanci ice cream custard ya fi soyuwa a wajen yara ƙanana.

Abubuwan da ake bukata
1. custard,
2. madara,
3. vanilla flavour,
4. sugar.
Yadda ake haɗawa,
1. ki dama custard da ruwan sanyi ki sheƙa ma da na zafi, ya yi kamar koko,
2. ki sa madara mai yawa a kai, da filabo da sugar, ki juya su sosai, su haɗe jikinsu,
3. ki bar shi ya huce, ki sa a fridge ki bar shi har dai ya yi ƙanƙara.

Domin sanin yadda boga ko biredin kwakwa danna nan

labarin da ya wuceSahabban Da Suka Fi Kowa Rawaito Hadisai
Labarin na GabaYadda ake Danbun Shinkafa
Babbar Dalibar addini, wacce ta karanci abin cei da lafiyar sa (food and nutrition) da kuma kwararriyar mai hada abin ci da kuma koyar da aikin hannu