Yadda Ake Gireba

0
2857

Gireba abin maƙwalashe ce, da ta samo asali daga fulawa; kuma ana yin ta ne da abubuwan amfanin yau da kullum, masu sauƙin samuwa. Ku dai ku biyo mu domin ku ga yadda za a yi wannan girebar.

Abubuwan haɗawa

Fulawa
Suga
Riɗi(kantu)
Man gyaɗa

Yanda ake haɗawa

1. Da farko uwar gida za ki tankaɗe fulawarki a roba mai ɗan faɗi. Sai ki jiƙa suganki.

2. Ki zuba man gyaɗa kaɗan, sai ki juya shi sosai, za ki ga ya yi wara-wara.
Sai ki ɗauko jiƙaƙƙen suga, ki kwaɓa fulawarki, kar ta yi ruwa, za ki yi shi kamar na cincin.

3. Ki ringa ɗiba kina sawa a hannunki, ki na dunƙulawa da ɗan faɗi, har ki gama.
Sai ki barbaɗa riɗi a kai, sai ki ɗauko tiren oven ɗinki, ki shafa man gyaɗa, sai ki jera ki sa a cikin oven ɗinki, ki gasa idan ya yi sai ki ɗauko ki kwashe. sai a ci.

Domin sanin Yadda Ake Cookies danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Gireba
Labarin na GabaYadda Ake Dambun Nama