Ko kun san:- gyasarar gyada na dauke da sinadarai masu gina jiki kamar protein, fiber, vitamin E, potassium, magnesium zamu iya sarrafagasarar gyada waje abinci kala kala kamar kunun gyada,sandwich ko kuma ana iya ci da biredi da sauransu.
Abubuwan bukata
-
Gyada mara ɓawo[kofi daya]
-
Gishiri
-
Barkono rabin karamin chokali
-
Chitta rabin kwatan karamin chokali 1/3.
Yadda ake hadawa
- A cikin tukunya mai zurfi a zuba gyada a soyata har sai tayi kalar ƙasa (wato golden brown)
- Sai a juye gyadar a matankadi a cire ɓawon jikin sannan a bakace har sai ta fita tas.
- A zuba kayan kamshi a ciki sannan a markada. Amma kar a saka ruwa
- Za a iya ci da biredi, ko yalon bello, sannan za a iya kunun dashi
- na iya yin kwado dashi ko kunun gyada nau’o’in abinci masu lafiya.