Tag: gyada

  • Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin groundnut sweet potato balls (groundnut cake) ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin ɗan Adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.

    Abubuwan Buƙata

    1. Soyayyar gyada ¼ cup
    2. Dankalin Hausa matsakaita
    3. Albasa a yanka Ƙanana ko a jajjaga
    4. Curry ½ tablespoon
    5. Markaɗaɗɗen nama
    6. Sinadarin ɗanɗano
    7. Attaruhu guda biyar jajjagge
    8. Tafarnuwa
    9. Breadcrumbs 1 cup
    10. Kwai 3 (a fasa a kaɗa shi)
    11. Man gyaɗa na suya

    Yadda ake haɗawa

    1. A cikin kwano mai kyau a zuba dafaffen dankali, sai a farfasa su, su fasu da kyau.
    2. Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin ɗanɗano, curry, thyme da nama a juya a hankali
    3. A samu dan faranti a ringa ɗiban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye
    4. A tsoma wannan ball cikin ƙwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe. Bon apetite

    Domin koyon  Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie  danna nan.

  • Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie

    Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin groundnut, sweet potato pie, ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san dankalin Hausa na ɗauke da sinadarin vitamin B,C,E da vitamin K wanda yake yaƙi da kwayoyin cuta a jikinmu.

    Abubuwan Buƙata

    Yadda za a haɗa pie                                           yadda za a yi Fillings
    1. fulawa kofi 2                                                   Dankalin Hausa guda ɗaya.
    2. Baking powder babban cokali ɗaya                   Gyaɗa ½ kofi
    3. Man gyada Albasa
    4. Gishiri ½ ƙaramin cokali                                  Attaruhu 2 matsaƙaita
    5. Ƙwai guda ƙaya (na shafawa kafin gashi)          Tafarnuwa 1
    6. Man suya                                                       Sinadarin ɗanɗano  guda1
                                                                            Thyme ½ rabin ƙaramin cokali
                                                                            Fulawa 2 cokali babba iyu
                                                                            Kori curry½ ƙaramin cokali

    Yadda ake haɗawa

    1. A cikin tukunya a zuba gyaɗa a dafa ta dahu da kyau, idan ta dahu sai a saka dankali, idan ya dahu, sai a tace su, a ajiye a gefe
    2. Cikin tukunya mara zurfi a zuba mai chokali biyu, a zuba albasa, a ɗan ba ta tsoro, sai a zuba attarahu tare da tafarnuwa da sinadarin ɗanddano, thyme da kori(curry) a juya na minti 1-2
    3. A zuba dankali da gyaɗa a ɗan juya
    4. A cikin ƙaramin kofi, a haɗa fulawa da ruwa ,sai a zuba cikin wannan haɗin dankali da gyaɗa dake wuta, sai a bar shi ya ɗan hade na minti biyu kafin a kashe wuta.

    Yadda zamu haɗa pie ɗinmu

    1. A murza fulawa da man gyaɗa sosai, sai a zuba ruwa da gishiri a murza, ya murzu da kyau, sai rufe shi na minti 5-7 domin ya haɗe da kyau
    2. Bayan wannan mintuna, sai a sake murza shi, sannan a yi rolling a sami meat pie cutter, in babu a sami ɗan roba ko kofi mai ɗan girma, sai a ringa yanka fulawa da shi circle-circle
    3. A zuba wanna hadin gyaɗa  da dankali a tsakiya, sai  a shafa ruwan fulawa a gefe sannan rufe, a danna cokali mai yatsu
    4. A shafawa pie din ruwan ƙwai
    5. A gasa na minti 30 ko sama ko kuma idan ya yi ruwan ƙasa wato golden brown.
  • Yadda Ake Kuli-Kuli

    Yadda Ake Kuli-Kuli

    Ko kun san:- kuli-kuli abincin yara ne ko ince yara nason Kuli Kuli kuma ana iya sarrafata ta hanya yin garin quli-quli sannan ya zama ingredients din abincin kowa.

    Abubuwan Bukata

    1. Gunda
    2. Gishiri
    3. Citta
    4. Barkono
    5. Sinadarindandano
    6. Sugar

    Yadda ake hadawa

    1. A soya gyada sama-sama sai barzata tabbatar an tsince an barza (babu mai bori kwata-kwata).
    2. A fitar da baqin gyada, domin tana saka daci
    3. Sai ka kai a markada kar a zuba ruwa kamar kullin gyada (peanut butter)
    4. A jiqa
    5. A tsince gyada, a cire mai bori sannan a cire bakin gyadar sai a soyata sama-sama karta qone
    6. A mar kada gyada dan gishiri, citta ko in mai sugar za’ayi sai an dan saka sugar.
    7. A tace ruwan tsamiya a barshi ya kwanta sai a juye abu mai kyau.
    8. Bayan an markada gyada, sai a sakata cikin kwano mai zurfi a zuwa wannan ruwan tsamiya kadan ayita juyawa da muciya ko cokalin katako har sai anga mai ya fara fitowa.
    9. Sannan za’aga gasarar ya curewa ko ince yana dunkulewa. Sai a tsiyaye mai sannan a cura qulin a soyata.
      Domin saninyadda ake kek din gyada danna nan
  • Yadda Ake Gasarar Gyada (Peanut Butter)

    Yadda Ake Gasarar Gyada (Peanut Butter)

    Ko kun san:- gyasarar gyada na dauke da sinadarai masu gina jiki kamar protein, fiber, vitamin E, potassium, magnesium zamu iya sarrafagasarar gyada waje abinci kala kala kamar kunun gyada,sandwich ko kuma ana iya ci da biredi da sauransu.

    Abubuwan bukata

    1. Gyada mara ɓawo[kofi daya]
    2. Gishiri
    3. Barkono rabin karamin chokali
    4. Chitta rabin kwatan karamin chokali 1/3.
    Yadda ake hadawa
    1. A cikin tukunya mai zurfi a zuba gyada a soyata har sai tayi kalar ƙasa (wato golden brown)
    2. Sai a juye gyadar a matankadi a cire ɓawon jikin sannan a bakace har sai ta fita tas.
    3. A zuba kayan kamshi a ciki sannan a markada. Amma kar a saka ruwa
    4. Za a iya ci da biredi, ko yalon bello, sannan za a iya kunun dashi
    5. na iya yin kwado dashi ko kunun gyada nau’o’in abinci masu lafiya.
    Domin sanin yadda ake coconut jollof rice danna nan