Yadda Ake Coconut Jollof Rice

0
1173

A yau za mu koyi yadda ake coconut jollof rice.

Abubuwan da ake buƙata:

  • Garin kwakwa ko markaÉ—aÉ—É—iyar kwakwa
  • Shinkafa
  • Karas
  • Koren tattasai
  • Koren wake Æ™anana (Peas)

Yadda ake haÉ—awa

  1. A dora ruwa a wuta. Idan ya tafasa, sai a zuba shinkafa har sai shinkafar ta tafasa na tsawon minti 15 sannan sai a wanke da ruwa a sa a matsami a ajiye.
  2. A kankare karas, sannan a wanke kafin a yayyanka shi ƙanana. A wanke tattasai da koren wake da koren kanana (Peas) sai a yayyanka su, amma ban da (Peas) din.
  3. Bayan an kankare bayan kwakwar an markada farin, sai a zuba ruwa sosai. Da ruwan kwakwar za ayi sanwar dahuwar.
  4. A zuba ruwan kwakwar a tukunya bayan ya tafasa sannan a zuba wannan ajiyayyen shinkafar idan ta kusa dahuwa, sai a zuba yankakken koren tattasai da karas da koren wake, da kuma koren wake ƙanana (Peas) a rufe da murfi a rage wutar girkin.
  5. Bayan mintuna biyar, sai a gauraya wannan shinkafar a sauke. Shi kenan an kammala.
  6. Ko da maigida ba mai son cin shinkafa ba ne, za ki ga ya fara sha’awar cin irin wannan girkin. Za a iya haÉ—a wannan girkin da miyar kaza ko miyar kifi.
Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan