KAYAN HAƊI
- Farin kifi 8 (dafaffe)
- Dankali 8 (dafaffe)
- Cokali 1 na kayan ƙ amshi.
- Cokali 1 na ruwan lemon tsami
- Ƙwai guda 1
- Butter cokali 1
- Tafarnuwa 1
- Abin ɗanɗano/ attaruhu da albasa
Domin karanta bayani akan Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauki Danna nan
Yadda za a haɗa
A ɗan daka dankali sama-sama sannan a sa kifi, a zare ƙayar, a daka tafarnuwa da kayan ƙamshi a haɗa da sauran gaba ɗaya da attaruhu da albasa duk a haɗa a cakuɗa su gaba ɗaya.
Daga nan sai a sa ɗanɗano, Sai a cuccura su gabaki ɗaya kamar ƙwallo, a ɗan barbaɗa fulawa a tsoma a ruwan kwai sannan a soya a ruwan mai mai zafi.
Domin karanta cikekken littafin Girke Girke Danna nan