KAYAN HAƊI
- Kifi
- Sinadarin ɗanɗano
- Gishiri
- Curry
- Mai
- Kayan miya
- Kanwa
Yadda za a haɗa
Da farko a soya mai da albasa a zuba yankakken tattasai da tumatir da albasa, a kawo ruwa kaɗan a zuba da ƴar kanwa, A gyara kifin a wanke a zuba, a saka gishri da maggi, ki bar shi kamar minti goma sai a sauke kana iya ci da shinkafa ko couscous da sauran su.