KAYAN HAƊI
- Ƙoda
- Hanta
- Nama
- Albasa
- Kayan ƙamshi
- Gishiri
- Sinadarin ɗanɗano
- Kayan miya
Yadda za a haɗa
A sami ƙoda da hanta da nama (na rago) duk sai ki tafasa ki yanka su ƙanana, sai ki samu albasa ki soya, ki kawo mai kaɗan ki zuba, in ya soyu ki zuba markaɗen kayan miyar nan, ki bar ta ta yi kauri,sai ki saka dankalin da naman a cikin miyar sannan kisa kayan ƙamshi idan ya dahu sai a sauke.