Yadda ake Danbun Shinkafa

0
1829

Abubuwan da ake buƙata a wajen haɗa danbun shinkafa ba su da yawa sosai, kuma abinci ne mai daɗin gaske musamaman a ce an kula wajen tsafta a lokacin da ake yin sa.

Abubuwan buƙata:

  1. Shinkafa
  2. Zogale
  3. Gyaɗa
  4. Attaruhu
  5. Albasa
  6. Mai
  7. Spices.

Yadda ake haɗawa:

Za ki kai shinkafarki(ba ta tuwo ba)a ɓarza miki a inji, sai ki tankaɗe, idan kuma ba gari sai ki turara ta, ki ajiye. zogalen ma ki turara shi ko ki dafa, sai ki daka gyaɗa kar tai laushi, attaruhunki ma haka, ki yanka albasa, sai ki haɗe su cikin shinkafarki, ki juya har su haɗe kisa maggi da spices ɗinki da mai kaɗan, saboda kar ya dunƙule. Sai ki maida, ki sake turarawa, idan ya dahu, za ki ji ƙamshi, sai ki sauke ,shi kenan. A ci daɗi lafiya.

Domin karanta yadda ake barabusku ko yadda ake tuwon masara danna koren rubutu

labarin da ya wuceYadda Ake Ice Cream Custard
Labarin na GabaYadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Ayaba da Kwakwa