Barkan mu da sake kasance a fanin girke-girkenmu na WikiHausa. A yau za mu koyi yadda cake mai kala uku.
Abubuwan da ake buƙata;
- Kwai 7
- Butter 1 (kimar leda 1)
- Baking powder ƙaramin cokali uku (2 tsp)
- Flavour ƙaramin cokali uku (1 stpn)
- Sikari kofi 1 (ko ki zuba iya zaƙin da zai miki)
- Food colour (shuɗi, kore da ruwan huda)
Yadda ake haɗawa
-Da farko ki tankaɗe fulawarki tare da baking powder.
-Ki yi sami mixer machine, ki sa buttarki a cikin wannan kwanonsa (ko ki sami wani kwano daban, idan da hand mixer za ki yi) ki yi ta motsa shi na ɗan wani lokaci.
-Sai kuma Ki kawo sikarin, ki sa a ciki, ki yi ta motsa shi har sai sikarinki ya narke a ciki, (wato ba ki jin gudajin sikari a cikin butter).
– Sai a ɗauko kwai ki fasa, ki motsa shi (kwan ana so ana sa shi ne ɗaya bayan ɗaya, kuma ana motsa shi, bayan kowane sa ƙwai ɗaya) har ki gama da ƙwan naki.
Sannan sai a ɗauko fulawarki da kika tankaɗe tare da baking powder (za ki iya raba fulawar gida 6) kina zubawa a hankali a cikin wannan haɗin butter, har ki gama da fulawar, kina motsa shi.
-Ki ɗauko kwano guda 4 ki raba ƙullinki gida uku.
-Kar a manta sai a ɗauko food colour ki diga a kowane kwano (ko wani kwano kala daban amma kar ki sa colour a ɗaya ).
-Shi za ki ajiye shi daban (wanda ba a sa colour ba) Ki juya ko wani kwano (kwano 3 ke nan) ajiye a gefe.
-Sannan kuma a ɗauko abin gashin (shape ɗin abun gashin ya zama shape na abun yin yankan doughnut) Sannan a cikin abin gashin za ki shafa mashi butter a ciki kaɗan, kafin ki zuba ƙullin cake ɗin).
-Daga nan sai ki zuba haɗin ko wani kullin shuɗi,ruwam hoda da kuma sai fari (a gefe daban-daban sai ki ɗan jijjiga container)A hankali (ba a so a cika shi don kar ya zube a lokacin gashi, ki sa su rabi-rabi ko ya ɗan fi rabi don ya yi gashi mai kyau).
Karin bayani
Idan ba ki da abin gashin za ki iya sawa a miki a maƙera da aluminum shape din Kamar na doughnut. Sannan kalar za ki iya amfani da ta ruwa ko ta gari kuma za ki iya canza duk kalar da kike so.