Tag: Cin Cin

  • Yadda Ake Bread-egg Toast A Sauƙake

    Yadda Ake Bread-egg Toast A Sauƙake

    Barkan mu da  kasancewa  a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu  koyi yadda ake bread-egg toast. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    Abubuwan haɗawa:
    • Bread (na alkama)
    • Ƙwai
    • Gishiri
    • Pepper (yaji)
    • Mai
    Yadda ake haɗawa:
    1. Da farko Uwar gida za ki fasa ƙwanki, sai ki sa ɗan gishiri da yaji, sai ki kaɗa.
    2. Ki tsoma bread ɗin a cikin ƙwai, sannan ki ɗora pan ɗinki mara zurfi, sai ki shafa mai da tissue paper ba a so mai ya yi yawa. Idan ya yi, sai ki juya ɗayan gefen, haka za ki ta yi har ki gama.
    3. A sha da lemo ko shayi ko kuma a saka a lunch box ɗin yara na makaranta.

    Domin koyan Yadda Ake Rainbow Cake Doughnut Sabon Salo  danna koren rubutu nan

  • Yadda Ake Rainbow Cake Doughnut Sabon Salo

    Yadda Ake Rainbow Cake Doughnut Sabon Salo

    Barkan mu da sake kasance a fanin girke-girkenmu na WikiHausa. A  yau za mu koyi yadda cake mai kala uku. 

    Abubuwan da ake buƙata;

    1. Kwai 7
    2. Butter 1 (kimar leda 1)
    3. Baking powder ƙaramin cokali uku (2 tsp)
    4. Flavour ƙaramin cokali uku (1 stpn)
    5. Sikari kofi 1 (ko ki zuba iya zaƙin da zai miki)
    6. Food colour (shuɗi, kore da ruwan huda)
    Yadda ake haɗawa

    -Da farko ki tankaɗe fulawarki tare da baking powder.

    -Ki yi sami mixer machine, ki sa buttarki a cikin wannan kwanonsa (ko ki sami wani kwano daban, idan da hand mixer za ki yi) ki yi ta motsa shi na ɗan wani lokaci.

    -Sai kuma Ki kawo sikarin, ki sa a ciki, ki yi ta motsa shi har sai sikarinki ya narke a ciki, (wato ba ki jin gudajin sikari a cikin butter).

    – Sai a  ɗauko kwai ki fasa, ki motsa shi (kwan ana so ana sa shi ne ɗaya bayan ɗaya, kuma ana motsa shi, bayan kowane sa ƙwai ɗaya) har ki gama da ƙwan naki.

    Sannan sai a ɗauko fulawarki da kika tankaɗe tare da baking powder (za ki iya raba fulawar gida 6) kina zubawa a hankali a cikin wannan haɗin butter, har ki gama da fulawar, kina motsa shi.

    -Ki ɗauko kwano guda 4 ki raba ƙullinki gida uku.

    -Kar a manta sai a ɗauko food colour ki diga a kowane kwano (ko wani kwano kala daban amma kar ki sa colour a ɗaya ).

    -Shi za ki ajiye shi daban (wanda ba a sa colour ba) Ki juya ko wani kwano (kwano 3 ke nan) ajiye a gefe.

    -Sannan kuma a ɗauko abin gashin (shape ɗin abun gashin ya zama shape na abun yin yankan doughnut) Sannan a cikin abin gashin za ki shafa mashi butter a ciki kaɗan, kafin ki zuba ƙullin cake ɗin).

    -Daga nan sai ki zuba haɗin ko wani kullin shuɗi,ruwam hoda da kuma  sai fari (a gefe daban-daban sai ki ɗan jijjiga container)A hankali (ba a so a cika shi don kar ya zube a lokacin gashi, ki sa su rabi-rabi ko ya ɗan fi rabi don ya yi gashi mai kyau).

    Karin bayani

    Idan ba ki da abin gashin za ki iya sawa a miki a maƙera da aluminum shape din Kamar na doughnut. Sannan kalar za ki iya amfani da ta ruwa ko ta gari kuma za ki iya canza duk kalar da kike so.

    KARANTAYadda ake special cin cin

  • Yadda Ake Special Cincin

    Yadda Ake Special Cincin

    Yadda ake special cin cin

    Abubuwan haɗawa
    1. Fulawa kofi Biyu Butter ɗaya
    2. Madarar gari cokali biyar da rabi
    3. Sikari cokali biyu da rabi
    4. Baking powder cokali daya da rabi
    5. Bawon lemon tsami cokali daya
    6. Cinnamon quater na cokali
    7. Gyadar miya guda biyu
    8. Kwai biyar
    9. Gishiri kadan
    10. Ruwa
    11. Vanilla flavour kadan

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki  tankaɗe Fulawa, ki sa a roba, ki sa baking powder, sikari, Cinnamon (powdered), gyadar miya ki daka, ki sa, ki sa gishiri, ɓawon lemon (lemon zest), ki juya su haɗe.
    2. Ki buga ƙwai ki sa, ki sa madara, vanilla flavour, ruwa kaɗan ki kwaɓa dough ki yi kneading bayan ya haɗe ki raba kashi uku.
    3. ki ɗauko chopping board ko tire ki sa kashi ɗayan, kiyi rolling, sai ki yanka da cutter, haka za ki yi wa sauran dough in, wanda kika yanka ya rage shi ma za ki ƙara kneading ki yi rolling ki yanka.
    4. Ki ɗaura mai a wuta, ki sa albasa kaɗan, ki soya manki, sai ki sa cincin ki soya.

    KARANTA Yadda ake SCOTCH EGG