Yadda Ake Springrolls

0
1386

A yau za mu koya muku yadda ake haɗa springrolls na mussaman. Springrolls abin taɓawa ne na mussamman, mai sauƙin narkewa a ciki wanda yake da saukin haɗawa. Ku biyo ni domin koyon yadda ake haɗa shi.

Abubuwan Da Ake Buƙata

1.Fulawa kofi 4.

2.Mai cokali 6.

3.Abin ɗanɗano (yadda kake so).

4.Kayan ƙamshi.

5.Man suya.

6.Cabbage da carrots.

Yadda Za a Haɗa

A kwaɓa fulawa da mai cokal 6, kisa ruwa kaɗan, yayi kamar kwaɓin cincin. Ki murza da abin murji ya yi fale-fale. Ki shafa musu mai ki ɗora ɗaya kan daya, kamar hawa hudu.

Sai kisa mu murfin tukunya ki kifa shi a kan wuta ki shafa mai a jiki, ki gasa kowanne ɓari minti 2. Ki raba su a hankali ba tare da ya yage ba. Ki gama gaba ɗaya, ki ajiye su a gefe.

Mu dawo kan nama mu zuba mai kaɗan a kasko, ya ɗan fara zafi sai musa naman a ciki muna juyawa. Idan ya kusa mu saka abin ɗanɗano da kayan kamshi.

Mu kara juyawa a kawo kabeji da aka yanka sirisiri da gogaggen karas a zuba. A cigaba da juyawa su yi laushi kaɗan, sai a sauke.

A ɗauko fulawa falle ɗaya a zuba kayan haɗi daga sama a naɗo daga farko, a sake naɗo gefe da gefe a naɗa kamar tabarma a liƙe da ruwan fulawa da haka har a gama da sauran fulawa. Sai a sa mai a kaskon suya mai yawa ya fara zafi sannan a zuba ana soyawa kamar guda 10, idan ya yi a kwashe asa wani har a gama.

Wannan shi ne Spring rolls.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls. da Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceAzumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja
Labarin na GabaHadisi Na Tara Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu