A yau za mu koyi yadda ake biskit cikin sauƙi
Abubuwan da ake bukata
-
Fulawa 2cups
-
Bota 1/2cup
-
Baking powder 1tspn
-
Icing sugar 1,1/2
-
Gishiri 1tspn
-
Madara 1tspn
Yadda ake haɗawa
-
A tankaɗe fulawa a kwano daban
-
Sai a zuba mata icing sugar a ciki
-
Sannan a zuba gishiri da baking powder a ciki
-
Sai a zuba bota a ciki, a juya su, har sai sun haɗe jikinsu
-
Sai a zuba madara a kai, a ci gaba da cakuɗa su, har sai sun haɗe jikinsu.
-
Sai a sa a kan faranti a bubbuɗa shi.
-
Sannan a kawo abu mai faɗi, amman rawun dai-dai girman da ake so
-
A yayyanka sai a sa a tsinke (thooth pick) a ɓuɓɓula samansa, sannan a gasa.
Domin karanta yadda ake yogurt ko ice cteam custard danna nan