Yadda Ake Chocolate Cake Na Musamman

0
2984

Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, A yau za mu koyi yadda ake chocolate cake na musamman. Tare da ni Hafsat Shettimah.

   Abubuwan haɗawa:
 • Fulawa kofi 2
 • Rabin butter 125g
 • Kwai 8
 • Sugar kofi 1
 • Cocoa powder kofi 1
 • Butter milk kofi 1
 • Baking powder  ½ chokali
 • Nescafe ɗaya (irin na sachet dinnan)
 • Vanilla flavour ½ chokali
 • Chocolate flaovour ½ chokali
 • Cinnamon ½ chokali

Yadda ake haɗawa:

 1. A kunna wutar abin gashi domin ya yi zafi. Pre-heat
 2. A sa fulawa, baking powder, cocoa powder a roba sai a juya a ajiye a gefe.
 3. A cikin wata robar mai zurfi a sa butter da sugar a yi ta juyawa idan akwai mixer, sai a yi amfani da ita, sai butter ta bugu da kyau (fluffy) sai a fasa ƙwai a ciki, sannan a ci gaba da juyawa sannan sai a zuba Nescafe da butter milk a kan kwaɓin naki, ki sa flavours, ki juya su haɗe.
  1. Sai ki ɗauko pan ki sa baking sheets, sannan ki zuba kamar rabin pan ɗinki sai a saka cikin oven wuta ta zama 180oc na minti 15 ko kuma idan kin ji ya fara ƙamshi sai ki saka tsinke mai kyau idan tsinken ya fito da kyau to cake ya gasu.
  2. In kina so chocolate naki ya yi moist, kada ki cika masa wutan sama .
  3. Bayan kin cire, ki bari ya sha iska kaɗan sai ki samu kwano ki zuba in ba a lokacin za a ci ba.

Donin koyan Yadda ake hada brownies na musamman danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceYadda Ake Chips Da Sauce Na Ƙundun kaza
Labarin na GabaMa’anar Daula A Harshen Hausa