Yadda Ake  Fanke (puff-puff) A Cikin Sauƙi

0
3879

Barkan mu da  kasancewa a fannin girke girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake Fanke (puff-puff) tare da ni Hafsat Shettima.

Abubuwan haɗawa
  1. Fulawa kofi 1
  2. Sugar 1/3 kofi
  3. Salt pinch
  4. Yeast chokali 1 teaspoon
  5. Mai (na suya)
 Yadda ake haɗawa
    1. A cikin roba mai zurfi, a zuba flour da yeast da sugar da ruwan ɗumi, ki kwaɓa ya kwaɓu sosai, ya yi ruwa-ruwa amma ba sosai ba, sai a rufe a wuri mai ɗumi.
  1. Ya sami kamar awa 1, idan ya yi, za ki ga ya tashi, sai ki ƙara buga shi.
  2. Sai a ɗora kasko a wuta, a sa mai ya yi zafi. sai a rinƙa ɗiban ƙullin da chokali ana sawa a cikin mai.
  3. A soyawa kuwa, ya yi jar suya.
Domin koyan Yadda ake bread-egg toast a sauƙake danna koren rubutun nan.

 

labarin da ya wuceYadda Ake Kebab Sabon Salo A Sauƙaƙe.
Labarin na GabaYadda Ake Samosa A Sauƙaƙe