Yadda Ake Haɗin Salat Na Gargajiya

0
2198

salat kayan ganye ne, kuma abinci ne mara nauyi. wanda yake ƙara lafiya, musamman waɗanda suke da matsalar narkewar abinci a cikin su da kuma masu son sassaita ƙiba da tafiyar jini a jika, domin koyan yadda ake haɗa shi, sai abi waɗannan matakai masu zuwa:

Abubuwan  da ake buƙata (kayan haɗi):

-Ganyen salat
-Nama ko kifi
-Dankalin Hausa
-Man gyada
-Koren tattasai
-Maggi, gishiri

  • farko sai a gyara salat ɗin
  • kar a yanka shi, sai an wanke.
  • Sannan a kaɗa ruwa da ɗan gishiri, a dinga tsoma shi ɗaiɗai, ana wankewa har a gama, sai a tsane shi.
  • Bayan haka, sai a yanka ganyen salat ɗin, manya amma ba fala-fala ba.
  • Sai a rufe ganyen salat ɗin a kwanon da iska tana iya shiga  kamar kwando.

A dafa nama da albasa da attaruhu da ɗan mangyada da maggi da gishiri da Dankalin Hausa a yanka shi Ƙanana, amma kada a bari ya laguɓe, sai a tsame shi a bar naman ya dahu ruwan ya tsotse a jikinsa, idan naman ya dahu a sauke shi a bari ya huce sai a yanka shi ƙanana a yanka koren tattasai, naman da dankalin sai a juya shi kamar yadda ake juya kwaɗo. (kifi shi ma haka za ai masa)

Sai a ɗauko ganyen salat ɗin nan da aka yanka, a zuba masa kayan hadin nan na nama ko kifi a juya, sai a zubacshi a kwano ko filet a jera shi domin ɗaukar ido.

Wannan shi ne yadda ake haɗin salat cikin sauƙi.

kada ki/ka manta za ki/ka iya turo mana da duk abin aka iya domin a ɗora shi a wannan shafin

domin turawa da abin aka iya danna koren rubutun nan.  

labarin da ya wuceYadda Ake Abincin Sallah Na Musamman
Labarin na GabaYadda Za Ka Mayar Da Gidanka Masarautarka