Yadda Za Ka Mayar Da Gidanka Masarautarka

0
1531

Tabbas namiji na iya zama shugaba mai cikakken iko a gidansa, muddin yana kwatanta halaye irin na shugaba nagari. Kuma yana kaucewa duk abin da zai kawo raini har sarautarsa ta kasa tasiri. Wato abubuwa irin su: Zalinci  da wulakanci da Zagi da kuma zargi.

Shi mai son wannan sarauta, dole ne ya fahimci cewa  ana samun kurakurai daga
kowacce irin mace, wacce za ka aura (budurwa/bazawara). Ko matarka da ka  riga ka aura. ƙarama ce ko babba, Malama ko kuma ɗaliba.

Saboda ajizanci na ɗan Adam (ba mala’ika ba ce) ga kuma yanayin yadda Allah Ya yi hallitar mata. Annabi (S.A.W) ya ce: “An halicci mata daga ƙashin haƙarƙari, wanda yake a karkace. Idan ka ce sai ka miƙar da ita, to sai ta karye , karyewar kuma ita ce sakin ta”.(Muslim)

A Matsayin ka na shugaba, dole sai kana haƙuri da afuwa. Za ka shimfiɗa sarautarka a gidanka har a dinga ma biyayya cikin farin ciki.

MATAKAI DA NAMIJI ZAI BI DOMIN ZAMA SARKI A GIDANSA.
1- KARANTAR ƊABI’UN MATA: Karantar irin halaye da ɗabi’un mata. Mace na son yabo da ziga. Musamman idan ta yi ƙunshi da kitso da girki da kwalliyya da tsaftace gida har ma da turare. Misali :”Kai Tabarakallah! Wannan kwalliya ta ƙara fito da kyawunki”. Shi kenan fa, za tai ta tunanin kullum ta burge ka. Ka ga ka yi nasarar zama Sarki.

2- JIN AURE IBADA NE: Duk ɗawainiyar da kake yi, za ka samu kyakkyawan sakamako a wajen Allah. Miji ya jajirce gwargwadon karfinsa wajen ciyarwa da tufatarwa da kiyaye mutuncin ta da magani . Wannan na daga cikin haƙƙin ta a kanka. Kuma manyan abubuwan dake ƙara wa miji daraja. Har a dinga rawar jiki na masa biyayya.

3- LULLUƁE MACE DA SOYAYYA: Yi ma ta maganganu masu daɗi. Yawan sumbatarta, da haɗa jiki da ita.

Duk da kasancewar Annabi (S.A.W) Shugaban wannan al’umma. Yana cin abinci da A’isha (R.A) ta ci. Yana kishingiɗa a kan cinyarta. Yana ba ta kansa ta taje masa. Yana wasan tsere. Yana wanka da iyalinsa. Duk waɗannan hadisai ne ingantattu.

Idan miji ya zama mai koyi da irin waɗannan kyawawan halaye, na rayuwar soyayya ta Annabi(S.A.W) zai sa ka mallaki zuciyar matarka. Ta zamo ma raƙumi da akala, sai yadda ka yi da abar ka.

4- ILMIN ZAMAN AURE: Na sa wa namiji ya zama yana da gogewa kan aure . Ka yawaita sauraron Nasihohin malamai daban-daban kan aure. Da halartar majalisan Malamai.

Bugu da ƙari, ka yi ƙoƙarin matarka ta samu Ilmin addini (zuwa islamiyya) .A nan za ta gane darajarka da shugabancinka, Allah ne ya naɗa ka. Allah Ya fada:… kuma maza su ne suke da daraja a kan mata”.( Baqara:228).

Ɗaukar nauyin ta, ta je taruka/wuraren koyon Ilmin aure. Zaburar da ita  kan yadda za ta zamo mai tarairayarnka. Da biyayya a fadarka.

5- KULAWA TA MUSAMMAN :  Bayar da kulawa a wasu keɓantattun yanayi/lokaci na Mace.

Misali : Lokacin da mace ta samu ciki. Wasu matan na yawan fushi da kwaɗayi da kasala da kuma rashin Lafiya .

Lokacin haila: Yawan ɓacin rai da sha’awa mai karfi da ciwon baya da kai da kuma Mara .

Sai ka daure ka ba ta kulawa ta musamman. Ba ta abubuwan da take buƙata. Da lallaɓata ta tsallake wannan yanayin. Ko ba komai dai  zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.

6- SHIMFIDƊAR MA’AURATA : Wannan al’amari babba ne sosai cikin aure. To ka ji inda sarki ke ajiye sarautarsa a gefe. Saboda ya tabbatar yana gamsar da matarsa cikin salo na wasanni da soyayya. Ya zama ya taimaka mata ga barin saɓa wa Allah(Zina). Hakan daraja ce da ƙimar mai gida . Wacce za ta sa a dinga masa fadanci da rawar jiki wajen masa biyayya.

7- TSAFTA :  Dabi’ar sarakai ce yawan tsaftar jiki da baki da kwalliya da ado da ƙamshi. Tabbas waɗannan muhimman abubuwa, suna sa namiji yai kyau. Koda kuwa a ce mummuna ne. Shi ya sa za ka ga ba a gajiya da kallon sarki.

Ka kula da yawan asuwaki don ta dinga samun natsuwar liƙe maka.

Assayida A’isha (R.A) ta ce : “Annabi(S. A. W) yana yin asuwaki a duk lokacin da zai shiga gida”.

Ƙazanta ta daɗe tana sa raini da ƙiyayya. A matsayin ka na shugaba, ƙazanta ba ta dace da kai ba. Tsaftarka za ta ƙara kwarjini a cikin shugabancinka, har ka zama sarkin zuciyar matarka.

Kafin in kammala dai, kasancewa a ɗan taƙaice na kawo su. Kuma bari in tuna mana cewar a kowacce fadar Sarki fa . Wazirin sarki na da matukar muhimmacin gaske. Matarka ita ce wazirinka. Duk da kasancewar ka shugaba, sai ka sakko da kanka. Ku dinga saita rayuwarku tare, illa iyaka madanni(remote control) yana hannunka.

A kodayaushe ka guji yawan hayaniya da zagi. Ka dinga sanya soyayya, jinƙai da tausayi. Tabbas sarautarka za ta yi tasiri. Saboda yin hakan shi ne fa’idar yin Aure.

Allah (SWT)  yake cewa :
“Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga masu yin tunani “.(Rum:21)

Wassalamu Alaikum. Allah Yai mana jagoranci.

labarin da ya wuceYadda Ake Haɗin Salat Na Gargajiya
Labarin na GabaYadda Ake Kulle Post Ɗin Da Bai Dace A Gani A Facebook Ba (Hide Post)
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.