Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin banana nutella sandwich, ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.
Abubuwan da ake buƙata
Biredi slice -6
Mai cokali 3
Kwai 1
Siga cokali 2
Nutella
Ayaba
Madara ½ kofi
Yadda ake haɗawa:
- A buga Ƙwai, sugar da madara a cikin kwano mai zurfi.
- A tsoma bread a ciki haɗin ƙwai, madara da sauran su, sai a shafa nutella a kan sashe ɗaya.
- A shirya ayaba a kai, sai a ɗauko wani ɓarin breadin a ɗora.
- A gasa a toaster in ya gasu sai a cire.