Tag: nutella

  • Yadda Ake Banana Nutella Sandwish

    Yadda Ake Banana Nutella Sandwish

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin banana nutella sandwich, ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Abubuwan da ake buƙata

    Biredi  slice -6

    Mai cokali 3

    Kwai 1

    Siga cokali 2

    Nutella

    Ayaba

    Madara ½ kofi

    Yadda ake haɗawa:

    1. A buga Ƙwai, sugar da madara a cikin kwano mai zurfi.
    2. A tsoma bread a ciki haɗin ƙwai, madara da sauran su, sai a shafa nutella a kan sashe ɗaya.
    3. A shirya ayaba a kai, sai a ɗauko wani ɓarin breadin a ɗora.
    4. A gasa a toaster in ya gasu sai a cire.

    Domin koyar yadda ake ice cream na ayaba danna wannan koren rubutun