A yau zamu koyi yadda ake masar dankalin turawa
Abubuwan da ake bukata
Yadda ake hadawa
- A fere dankali, sai a dora shi a wuta ya nuna ya yi luguf sosai.
- Sannan sai a dauko roba ko kwano mai zurfi a zuba a ciki.
- A debo kwai mai dan dama a fasa a kan dankalin.
- Sai a samu ludayi a dama dankalin da kwan har sai sun hadu sosai.
- Sai a debo albasa da attarugu a jajjaga su sannan a zuba a kan hadin dankalin da magi da gishiri da kori daidai kayan dandano,
- Kuma annan a sake dama hadin domin kayan hadin su shiga dankalin sosai.
- A dauko tanda a dora a kan wuta, a zuba man gyada a kowane gida sannan a debo kullun dankalin a zuba a kowane gidan tandar.
- Sai a dan ba shi mintuna domin dahuwar cikin masar, idan gefe daya ya yi, sai a sake juya wainar zuwa dayan gefen har sai ta nuna kafin a sauke daga wuta
Domin sanin yadda ake lemon ardeb danna nan