Yadda Ake Egg French Toast

0
1299

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa,

wand muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na

ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

A yau, za mu koyar da yadda ake yin EGG FRENCH TOAST ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

Abubuwan buƙata

  1. Biredin alkama yanka 4
  2. Fulawa ½ kofi
  3. Ƙwai
  4. mai cokali 3 (domin shafa abun suya)
  5. Sinadarin Ɗanɗano
  6. yaji

Yadda ake haɗawa

  1.   A cikin buɗaɗɗen kwano, a zuba, fulawa, sinadarin ɗandano da ɗan barkono, a juya a    ajiye gefe, a wani kwano mai ɗan zurfi sai a kaɗa ƙwai shi ma, a jiye gefe guda.
  2.  A ɗauko wannan bread, sai a tsoma a cikin ruwan ƙwai, sai a saka shi cikin flour,  sannan a mayar cikin ruwan ƙwai, a fito da shi.
  3.  A ɗora abun suya mara zurfi, sai a shafa mai a kai, sannan a saka bread ya gasu, na minti 1-2 ko in launinsa ya koma golden brown.

Domin koyar Yadda ake caramelized onion grilled cheese sandwich dan wannan koren rubutun

 

 

labarin da ya wuceYadda Ake Caramelized Onion Grilled Cheese Sandwich
Labarin na GabaYadda Ake Banana Da Strawberry Smoothy