Tag: french toast

  • Yadda Ake Egg French Toast

    Yadda Ake Egg French Toast

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa,

    wand muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na

    ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau, za mu koyar da yadda ake yin EGG FRENCH TOAST ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Abubuwan buƙata

    1. Biredin alkama yanka 4
    2. Fulawa ½ kofi
    3. Ƙwai
    4. mai cokali 3 (domin shafa abun suya)
    5. Sinadarin Ɗanɗano
    6. yaji

    Yadda ake haɗawa

    1.   A cikin buɗaɗɗen kwano, a zuba, fulawa, sinadarin ɗandano da ɗan barkono, a juya a    ajiye gefe, a wani kwano mai ɗan zurfi sai a kaɗa ƙwai shi ma, a jiye gefe guda.
    2.  A ɗauko wannan bread, sai a tsoma a cikin ruwan ƙwai, sai a saka shi cikin flour,  sannan a mayar cikin ruwan ƙwai, a fito da shi.
    3.  A ɗora abun suya mara zurfi, sai a shafa mai a kai, sannan a saka bread ya gasu, na minti 1-2 ko in launinsa ya koma golden brown.

    Domin koyar Yadda ake caramelized onion grilled cheese sandwich dan wannan koren rubutun