Abubuwan da ake buƙata
- Abarba
- Ruwan sanyi
- Sikari
- Na’ana
- Ɗanyar citta
- Ruwan lemon tsami
Yadda ake haɗawa
1. Da farko za ki ɓare abarba, ki yanka ta ƙanana, ki sa a blender, ki sa ruwan sanyi, sikari, ɗanyar citta ki niƙa su, ki tace.
2. Sai ki samu serving glass, ki dan daka na’ana, ki zuba pineapple juice da ruwan lemon tsami kaɗan ki juya. A sha lafia.
Karin bayani
Ba lallai sai da ruwan sanyi za ki yi ba, za ki iya amfani da ƙanƙara ko kuma bayan kin tace ki sa a firji ya yi sanyi.
In ba ki da na’ana za ki iya yin sa haka, haka shi ma lemon tsami. Wannan shi ne yadda ake haɗa lemon abarba a sauƙaƙe.
Domin karanta Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga danna nan.