Yadda Ake Haɗa Lemon Gyaɗa, Shinkafa Da Dankalin Hausa (Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake)

0
1270

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah.

A yau zamu koyar da yadda ake yin lemon gyaɗa, shinkafa da dankalin Hausa (groundnut, rice, sweet potato shake) ku biyo ni a sannu, domin mu koya tare……

Ko kun san Gyaɗa na da sinadarin minerals kamar su copper, manganese, potassium, calcium, iron, magnesium, zinc da kuma selenium wanda suke ƙara ƙarfin ƙashi da haƙori.

Abubuwan Buƙata

 1. Shinkafa ½ rabin kofi
 2. Gyaɗa ½ rabin kofi
 3. Dankalin Hausa
 4. Gyaɗa soyayyiya
 5. Siga
 6. Madara

Yadda Ake Haɗawa

 1. A wanke shinkafa a jiƙa ta, sai ta yi laushi.
 2. A fere dankalin Hausa a yayyanka.
 3. A soya gyaɗa a busar da ita.
 4. Sai a haɗe gyaɗa, dankali da kuma jiƙaƙƙiyar shinkafa a markaɗa a tace da abun tata.
 5. A raba ruwan gyaɗa biyu, a ɗora a wuta har sai ya yi kauri (kamar kunun gyaɗa). Sai a sauke a haɗe da ragowar ruwan gyaɗar, a saka madara da siga. Za a iya ƙara ruwa daidai kaurin da ake so.
 6. Za a iya tace shi da rariya, idan ya yi gudaji-gudaji, sai a saka a fridge ya yi sanyi.
 7. Asha lafiya.
labarin da ya wuceYadda Ake Biskit Ɗin Gyaɗa (groundnut cookies)
Labarin na GabaYadda Ake Groundnut Sweet potato Pie