Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Kufta su ne:
- Niƙaƙƙen nama
- Abin ɗanɗano
- Tafarnuwa
- Shammar
- Masoro
- Gishiri
Kayan Aiki
- Murhu/Risho/Gas
- Kasko
- Mazubi (mai tsafta)
- Cokali
- Abin daka
Yadda Ake Haɗawa
Za a niƙa nama dai-dai yadda ake buƙata, sai a sa masa abin ɗanɗano daidai yadda yai miki, ki sa shamma da tafarnuwa da kuma masoro, sai a zuba gishiri kaɗan, sai a haɗa da mai kaɗan, a cakuɗa, ya haɗa jikinsa.
Sai a riƙa cirar naman ana cuccurawa ko duddunƙulawa, dogo–dogo, sai a soya a mai me zafi.
Miyar da Ake Ci Da Kufta
Za a iya yi masa miya a ci da ita, a samu markaɗe na tumatur mai yawa, tattasai kaɗan, sai ki zuba a tukunya, ki sa masa ‘yar kanwa, ki sa mai, a sa masa tafarnuwa (dakakkiya), a sa abin ɗanɗano a bar ta ta yi kauri kamar faten doya, sai a sa naman a ciki ya yi minti 1 ko 2, sai a sauke za a iya ci da dogon biredi ko shinkafa ko taliya.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gima Macaroni Jallof danna nan