Tag: abinci mai gina jiki

  • Yadda Ake Macaroni 2

    Yadda Ake Macaroni 2

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Macaroni su ne:

    • Albasa
    • Tumatir
    • Green beans (koren wake)
    • Potatoes (dankali)
    • Niƙaƙƙen nama
    • Abin ɗanɗano
    • Vinegar (khal)
    • Kasbara
    • Shammar

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Tukunya
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Ludayi
    • Abin daka
    • Wuƙa

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami albasa, tumatir, koren wake, duk a yi slicing ɗin su, sai a yanka dankali ƙanana, a soya sai a ajiye shi a gefe; sai a sa mai daidai ƙima a tukunya, ki zuba minced meat (niƙaƙƙen nama) a ciki, a soya kar ya yi ƙarau, a zuba albasa da tumatir a ci gaba da juyawa. Sai a soya green beans da ɗan mai kaɗan, in miyar ta dahu a zuba abin ɗanɗano a zuba dankalin, a sa shammar da kasbara ta ƙara dahuwa kaɗan sai a sauke a ci da macaroni fara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Shinkafa Mai Ƙwai danna nan

    Dominn karanta bayani akan Mene Ne Abinci A Lafiyance? danna nan

  • Yadda AkeTherapeutic Food (abincin yara)

    Yadda AkeTherapeutic Food (abincin yara)

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake Abincin yara (therapeutic food) ku biyo ni a sannu domin mu koya  tare.

    Ko kun san yara masu cutar yunwa (tamowa) idan ana ba su wannan zai ƙara musu kuzari da kumari a jikinsu?

    Abubuwan Buƙata

    1. Gyaɗa (kofi biyu)
    2. Waken suya (kofi biyu)
    3. Dawa (kofi shida)
    4. Siga
    5. Madara (in ana buƙata).

    Yadda ake haɗawa

    1. A soya gyaɗa a bushe ta, sannan a niƙa
    2. A soya waken (soya beans) shi ma a niƙa
    3. Dawa ita ma a soya ta, sannan a niƙa
    4. Cikin roba mai kyau a haɗa dukkanin garin (wake soya, dawa da kuma gyaɗa ) a juya da kyau sai a sami leda mai kyau a juye a cikin sannan a saka a roba mai murfi a rufe. Duk sanda za a yi sai a ɗiba.

    Yadda ake haɗa kunun.

    • A ɗora tukunya mai zurfi, sannan a zuba ruwan zafi kaɗan yadda zai isa (kamar talge).
    • A ɗan kofi ko roba, a ɗebi garin kunun yara sai a zuba ruwa a cikin ɗan kadan a dama.
    • Idan ruwan ya tausa (tafasa) sai a zuba wannan gasarar kunun a cikin ruwan, a yi ta juyawa har sai ya yi kauri
    • Za’a iya saka madara domin ƙarin daɗi kuma za a iya sha a haka.

    Domin Yadda Ake Gasarar Gyada (Peanut Butter) danna nan