Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake tare da ni Hafsat Shettimah.
A yau zamu koyar da yadda ake yin donut na gyaɗa. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san kwaɓin biredi da doughnut iri ɗaya ne?
- Idan dough ɗin ya tashi, sai a sami chopping board da rolling pin; ana gutsurar wannan dough ɗin ana sake murza shi sai a saka donut cutter a yanka.
- A ɗora mai a wuta, idan ya yi zafi, a saka wannan donut ɗin; idan ya yi golden brown sai a juya ɗaya ɓarin.
- Idan dukkannin ɓarin sun soyu, a kwashe a matsami, za a iya sha da lemo ko shayi.
Domin sanin Yadda Ake Biredin Gyaɗa danna nan