A yau za mu koyi yadda ake gurasar tukunya, gurasar tukunya abinci ne da ake yin sa daga fulawa, gurasa na da sauƙin sarrafawa da sauƙin ajiya.
Abubuwan da ake buƙata:
- Fulawa
- Yis
- Kantu/riɗi
- Sikari
- gishiri
Yadda ake haɗawa
- A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa,
- Ka da a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
- Idan ana son gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a wajen kwaɓin.
- Sai a sami tukunyar ƙarfen mai ƙwari, a ɗora ta a kan wuta, idan ta yi zafi sosai, sai a zare itatuwan a bar garwashin, saboda ka da gurasar ta kone.
- Sai a cura gurasar a faɗaɗa ta, a saka cikin tukunyar,
- Idan an gama, sai a kawo murfi a rufe. Idan ta yi, za a ji ta fara ƙamshi.
Domin sanin Yadda Ake Gurasa Tanderu danna nan