Yadda Ake Gurasar Tanderu

0
1875

A yau za mu koyi yadda ake gurasar tanderu.

Gurasa abinci ne da ake yin sa daga fulawa, ya samo asali ne daga abincin Larabawa, gurasa abinci ne dake da matuƙar daɗi, da sauƙin sarrafawa da kuma dauƙan lokaci ba tare da ta yi komai ba. Ana iya cin gurasa da abubuwa da ya samu, musamman ma gurasar tanderu ta fi daɗi, domin tanderu tukunya ce, wadda ake ginawa da ƙasa, kuma duk abin da aka yi shi a cikin tukunyar ƙasa ƙamshinsa daban yake.

Abubuwan Da Ake Buƙata:

  • Fulawa
  • Yis
  • Kantu/ridi
  • Sikari
  • gishiri

Yadda Ake Haɗawa

  1. A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa.
  2. Kada a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
  3. Idan ana son Gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a cikin kwaɓin; idan kuma mai gishiri ce, sai a zuba gishiri a cikin kwaɓin.
  4. Idan lokacin zafi ne, za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so; awa uku zuwa huɗu ya ishe shi ya tashi.
  5. Amma idan lokacin sanyi ne yakan daɗe bai tashi ba. Idan ana so a yi gurasa da safe; to sai a kwaɓa fulawar tun da daddare.
  6. Idan an tabbatar kwaɓin ya tashi, sai a zuba karare a cikin tanderu, a kunna wuta domin tanderun ya yi zafi.
  7. Idan an tabbatar tanderun ya yi zafi sosai, kuma karan ya cinye sai a yayyafa ruwan kanwa a ciki.
  8. A saka tsintsiya a share toka-tokar da ta maƙale a cikin tanderun.
  9. Sai a kawo kwaɓin a cura shi ya yi faɗi, a faɗaɗa da hannu, yadda dai ake son fadinta ya kasance.
  10. Idan kina son kantu/ridi sai a zuba ɗan kaɗan a kan gurasar a tsakiya; idan kuma ba a so, shi kenan sai kawai a saka curin da aka yi a cikin tanderun.
  11. Idan an gama sakawa, sai a kawo tire a rufe tanderun. Takan ɗauki kamar minti ashirin zuwa ashirn da biyar kafin ta yi.
  12. Ba ma sai an kalli agogo ba, da ta yi za a ji ƙamshi ya turare ko’ina a gidan.
  13. Sai a kawo wuƙa da tire, a ringa saka wuƙa ana ɓamɓaro ta tana faɗawa kan tiren. Amma sai an yi a hankali saboda zafi, kada a ƙone domin tanderu yana da zafi sosai.

Domin sanin Yadda Ake Yogofriut danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Chocolate Milkshake
Labarin na GabaYadda Ake Gurasar Tukunyar Ƙarfe
Khadija Yusha'u (Amira)
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.