Tag: gurasa

  • Yadda Ake Bandashe

    Yadda Ake Bandashe

    A yau za mu koyi yadda ake bandashe.

    Bandashe abinci ne da ake yin sa daga gurasa, yana da sauƙin sarrafawa da daɗin ci, musamman ma a wajen karɓar baƙi da wuraren taruka.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Gurasa mai gishiri
    • Dakakken ƙuli-ƙuli
    • Albasa
    • Tumatir
    • Mai

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A sami gurasa a saka ta a cikin ruwan ɗumi, ta yi kamar sakan biyar a ciki sai a cire.
    2. A tsanar da ita, ko kuma a turara ta, abin da dai ake so shi ne, gurasar ta yi laushi sosai.
    3. Sai a zuba mai gaba da bayanta, sai ki kawo ƙuli-ƙuli a barbaɗa, shi ma gaba da baya; sai ki yanka tumatir da albasa da cocomba, idan ana so ma har kabeji ana iya sawa a kai.
    4. Idan ana buƙata ana iya kara mai, domin ya ji, a tabbatar ƙuli-kulinki ya ji magi; ba sai an zo ana ƙarawa a kai ba, ba zai taɓa yi ba.

    Domin sanin Yadda Ake Gurasar Oven danna nan

  • Yadda Ake Gurasar tanderun Nasara (OVEN)

    Yadda Ake Gurasar tanderun Nasara (OVEN)

    A yau za mu koyi yadda ake gurasar tanderun Nasara (Oven).

    Abubuwan da ake buƙata

    • Fulawa
    • Yis
    • Kantu/riɗi
    • Sikari
    • gishiri

    Yadda ake haɗawa

    1. A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa,
    2. Ka da a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
    3. Idan ana son gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a wajen kwaɓin
    4. Sai a tabbatar an kunna (oven) din ya yi zafi sosai, sai a kawo tiren gashi a shafa masa bota.
    5.  Sai a kawo kwaɓin a cura, a kuma fakada, sai a saka a cikin tiren gashi,
    6. Idan an saka duka, ko kuma iya yadda zai dauka, sai a mayar da tiren cikin (oven) din a rufe.
    7. Zai ɗauki kamar minti goma sha biyar, zuwa minti ashirin kafin ta yi. Ko kuma da an fara jin ƙamshi to ta yi, sai ki cire.

    Domin sanin Yadda Ake Gurasar Tukunya danna nan

  • Yadda Ake Gurasar Tukunyar Ƙarfe

    Yadda Ake Gurasar Tukunyar Ƙarfe

    A yau za mu koyi yadda ake gurasar tukunya, gurasar tukunya abinci ne da ake yin sa daga fulawa, gurasa na da sauƙin sarrafawa da sauƙin ajiya.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Fulawa
    • Yis
    • Kantu/riɗi
    • Sikari
    • gishiri

    Yadda ake haɗawa

    1. A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa,
    2. Ka da a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
    3. Idan ana son gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a wajen kwaɓin.
    4. Sai a sami tukunyar ƙarfen mai ƙwari, a ɗora ta a kan wuta, idan ta yi zafi sosai, sai a zare itatuwan a bar garwashin, saboda ka da gurasar ta kone.
    5. Sai a cura gurasar a faɗaɗa ta, a saka cikin tukunyar,
    6. Idan an gama, sai a kawo murfi a rufe. Idan ta yi, za a ji ta fara ƙamshi.

    Domin sanin Yadda Ake Gurasa Tanderu danna nan

  • Yadda Ake Gurasar Tanderu

    Yadda Ake Gurasar Tanderu

    A yau za mu koyi yadda ake gurasar tanderu.

    Gurasa abinci ne da ake yin sa daga fulawa, ya samo asali ne daga abincin Larabawa, gurasa abinci ne dake da matuƙar daɗi, da sauƙin sarrafawa da kuma dauƙan lokaci ba tare da ta yi komai ba. Ana iya cin gurasa da abubuwa da ya samu, musamman ma gurasar tanderu ta fi daɗi, domin tanderu tukunya ce, wadda ake ginawa da ƙasa, kuma duk abin da aka yi shi a cikin tukunyar ƙasa ƙamshinsa daban yake.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Fulawa
    • Yis
    • Kantu/ridi
    • Sikari
    • gishiri

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa.
    2. Kada a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
    3. Idan ana son Gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a cikin kwaɓin; idan kuma mai gishiri ce, sai a zuba gishiri a cikin kwaɓin.
    4. Idan lokacin zafi ne, za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so; awa uku zuwa huɗu ya ishe shi ya tashi.
    5. Amma idan lokacin sanyi ne yakan daɗe bai tashi ba. Idan ana so a yi gurasa da safe; to sai a kwaɓa fulawar tun da daddare.
    6. Idan an tabbatar kwaɓin ya tashi, sai a zuba karare a cikin tanderu, a kunna wuta domin tanderun ya yi zafi.
    7. Idan an tabbatar tanderun ya yi zafi sosai, kuma karan ya cinye sai a yayyafa ruwan kanwa a ciki.
    8. A saka tsintsiya a share toka-tokar da ta maƙale a cikin tanderun.
    9. Sai a kawo kwaɓin a cura shi ya yi faɗi, a faɗaɗa da hannu, yadda dai ake son fadinta ya kasance.
    10. Idan kina son kantu/ridi sai a zuba ɗan kaɗan a kan gurasar a tsakiya; idan kuma ba a so, shi kenan sai kawai a saka curin da aka yi a cikin tanderun.
    11. Idan an gama sakawa, sai a kawo tire a rufe tanderun. Takan ɗauki kamar minti ashirin zuwa ashirn da biyar kafin ta yi.
    12. Ba ma sai an kalli agogo ba, da ta yi za a ji ƙamshi ya turare ko’ina a gidan.
    13. Sai a kawo wuƙa da tire, a ringa saka wuƙa ana ɓamɓaro ta tana faɗawa kan tiren. Amma sai an yi a hankali saboda zafi, kada a ƙone domin tanderu yana da zafi sosai.

    Domin sanin Yadda Ake Yogofriut danna nan.