Tag: Abin ci

  • Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin groundnut sweet potato balls (groundnut cake) ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin ɗan Adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.

    Abubuwan Buƙata

    1. Soyayyar gyada ¼ cup
    2. Dankalin Hausa matsakaita
    3. Albasa a yanka Ƙanana ko a jajjaga
    4. Curry ½ tablespoon
    5. Markaɗaɗɗen nama
    6. Sinadarin ɗanɗano
    7. Attaruhu guda biyar jajjagge
    8. Tafarnuwa
    9. Breadcrumbs 1 cup
    10. Kwai 3 (a fasa a kaɗa shi)
    11. Man gyaɗa na suya

    Yadda ake haɗawa

    1. A cikin kwano mai kyau a zuba dafaffen dankali, sai a farfasa su, su fasu da kyau.
    2. Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin ɗanɗano, curry, thyme da nama a juya a hankali
    3. A samu dan faranti a ringa ɗiban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye
    4. A tsoma wannan ball cikin ƙwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe. Bon apetite

    Domin koyon  Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie  danna nan.

  • Yadda Ake Ajiye Kayan Miya Tsawon Shekara

    Yadda Ake Ajiye Kayan Miya Tsawon Shekara

    A yau za mu koyi yadda ake ajiye kayan miya tsawon shekara.

    Abubuwan da ake bukata:

    • TUMATUR
    • ATTARUHU
    • TATTASAI

    Yadda ake yi shi ne:

    1. Da farko za a samu kwalabar bama wato mayonnaise amma a tabbata akwai wani kwali a saman murfin
    2. Za a wanke a gyara su tsaf a markaɗa su
    3. Za a samu colander babba a zuba kayan miyan a daura  a kan bokiti domin ruwan kayan miyan ya tsane ko ya ragu saboda samun sauki wajen dahuwar ruwan zai tsotse da wuri
    4. Sai a zuba kayan miyar a bar shi yai ta dahuwa
    5. A ringa juyawa lokaci zuwa lokaci har sai ruwan kayan miyan ya gama ƙonewa baki ɗaya
    6. Su sai a ringa ɗiba a kan wutar, kada a sauke
    7. A ringa diba ana zubawa a cikin kwalbar ana jijjigawa domin yai kasa sosai kada a bar wata iska a ciki, har sai ya yi ciki.
    8. A danna da ludayi sosai ya cika bam sai a ɗauki murfin a rufe sosai
    9. Haka za a yi ta yi har a gama.
    10. Za a daura ruwa a wata tukunyar a dafa shi, amma kada ya tafasa sai a zuba kwalaban a cikin baho a kwara ruwan zafin a rufe kmar 1 hour sai a cire su a ajiye a kitchen ko cikin drowers ko a kasa ma duk dai inda ake so a ajiye
    Domin sanin yadda ake madarar yogurt danna nan
  • Yadda Ake Haɗin Yaji

    Yadda Ake Haɗin Yaji

    Barkan mu da sake kasancewa cikin shirinmu na girka-girken WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu a jikin ɗan Adam cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah. A Yau za mu koyar da yadda ake Haɗin yaji na musamman, ku biyo ni domin mu koya tare.

    Yadda ake Haɗin Yaji Na Musamman

    Abubuwan da ake buƙata

    Barkono
    Citta
    Kanumfari
    Masoro
    Kirfa (Cinnamon)
    Tafarnuwa

    Gyadar miya (Nutmeg)
    Ƙuli-ƙuli
    Sinadarin Ɗanɗano

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A gyara komai a fitar da datti.
    2. A daka komai daban-daban, a tankaɗe su, sai a haɗe su, a zuba sinadarin ɗanɗano a ƙara dakawa har su hade jikinsu.
    3. A adana yaji a mazubi mai kyau, mai murfi.

    Domin sanin yadda ake dambun nama danna nan

  • Yadda Ake Egg Sandwich

    Yadda Ake Egg Sandwich

    A yau  mu koyi yadda ake yin  EGG SANDWICH

    Wannan abincin  ya samo asali ne daga biredi, ga sauƙi wurin yi, kuma ga daɗi. daɗin daɗawa kuma, ga amfani a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan buƙata:

    Bread ( Mai yanka-yanka)
    Kwai
    Butter
    Tumatur

    Yadda ake haɗawa:

    Za a dafa ƙwai, a yanka shi irin yankan nan mai faɗi, shima tumatur ɗin a yanka shi irin yadda aka yanka ƙwan, a shafa butter a jikin biredin, sai a saka ƙwan, sai a sa kan tumatur sai a ɗauko wani biredin a daura a kan shi, sai a gasa shi a cikin abin gasawa, tsawon minti ɗaya ya gasu, sai a fiddo shi, za ki iya ci da tea.

  • Yadda Ake Plantain Chips Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Plantain Chips Cikin Sauƙi

    Yadda ake plantain chips
    To ga yadda ake plantain chips kamar haka dalla dalla:

    Abubuwan haɗawa

    1. Ɗanyar plantain
    2. Gishiri kaɗan
    3. Mai

    Yadda ake haɗawa

    1. Ki samu ɗanyar plantain ki yanka ta falan-falan.

    Sai ki barbaɗa gishiri kaɗan, ki juya ko’ina ya ji.

    1. Ki ɗaura mai a kan wuta, in ya ɗan yi zafi, sai ki zuba ki soya, in ya yi, sai ki tsane.

    KU KARANTA Yadda ake kosai mai laushi

  • Yadda Ake Special Cincin

    Yadda Ake Special Cincin

    Yadda ake special cin cin

    Abubuwan haɗawa
    1. Fulawa kofi Biyu Butter ɗaya
    2. Madarar gari cokali biyar da rabi
    3. Sikari cokali biyu da rabi
    4. Baking powder cokali daya da rabi
    5. Bawon lemon tsami cokali daya
    6. Cinnamon quater na cokali
    7. Gyadar miya guda biyu
    8. Kwai biyar
    9. Gishiri kadan
    10. Ruwa
    11. Vanilla flavour kadan

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki  tankaɗe Fulawa, ki sa a roba, ki sa baking powder, sikari, Cinnamon (powdered), gyadar miya ki daka, ki sa, ki sa gishiri, ɓawon lemon (lemon zest), ki juya su haɗe.
    2. Ki buga ƙwai ki sa, ki sa madara, vanilla flavour, ruwa kaɗan ki kwaɓa dough ki yi kneading bayan ya haɗe ki raba kashi uku.
    3. ki ɗauko chopping board ko tire ki sa kashi ɗayan, kiyi rolling, sai ki yanka da cutter, haka za ki yi wa sauran dough in, wanda kika yanka ya rage shi ma za ki ƙara kneading ki yi rolling ki yanka.
    4. Ki ɗaura mai a wuta, ki sa albasa kaɗan, ki soya manki, sai ki sa cincin ki soya.

    KARANTA Yadda ake SCOTCH EGG