Matsayin Koke-koke Da Kururuwa

0
268

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da Imaman Ahlul Baiti sun yi hani ƙaƙƙarfa a kan yin koke-koke da kururuwa saboda wata mutuwa ko wata musiba.

Ga kaɗan daga cikin ruwayoyin ingantattu kan haka daga littatafan shi’a:

1- Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Kururuwa ya yin mutuwa aiki ne na jahiliyya”.
2- Imamus Sadik (Alaihis Salam) ya ce: “Bai kamata a yi kururuwa ba ga wani mamaci, bai halatta ba, amma mutane, ba sa sani”.
3- Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Sautuka biyu tsinannu ne ,Allah yana ƙin su, su ne kururuwa lokacin musiba, da waƙa lokacin samun ni’ima”.

Ruwayoyi masu ɗauke da irin wannan saƙo da hana kira lokacin kowacce irin mutuwa ko musiba daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Ahlul Baiti suna da yawa za ka iya samunsu a waɗannan littatafan:

– Wasa’ilus shi’ana Hurrul Amilij.2 sh. 915.
– Jami’u Ahadisu shi’a-na Husaini Burujardi j. 3sh. 3sh. 488
– Biharul Anwar na Majlisi-j. 82 sh. 103.
– Mustadrakul Wasa’il na Nuri Attabrasi J. 1 sh.144.
– Alkafi na Kulaini j.3 sh. 325 da sauran su.

Waɗansu su ma daga cikin malaman nasu sun ce, babu wani saɓani a kan haramcin yin hakan kamar su:

Muhammad bin Makki Al-amili, da Muhammadul Husaini Al-shirazi da sauran su.

Domin karanta cikakken bayani a kan Haramcin Marin Fuska Da Dukan Ƙirji Da Zubar Da Jini danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ba Su Inganta Ba Game Da Ashura danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceTarihin Dutsen Dala Da Rayuwa A Kewayensa
Labarin na GabaAbin Lura Idan ‘Ɗan Ka Ko ‘Yar Ka Sun Kai Shekarun Farko Na Tashen Balaga