Yadda Za Mu Yi Koyi Da Annabi (S.A.W) A Dukkanin Tsare-tsaren Rayuwa

0
600

Duk wanda ya ce shi musulmi ne, to lallai ne abin koyinsa ya zamo Manzon Allah (S.A.W), a dukkanin tsare-tsare na rayuwarsa.

Misali: Tsarin Ilmi, tsarin zamantakewa, tsarin tattalin arziƙi, tsarin siyasa (shugabanci) da tsarin shari’ah. Abin nufi a nan shi ne, duk waɗannan tsare-tsare na rayuwa, su zamo a kan tsarin Alƙur’ani da sunnah, bisa fahimtar magabata na ƙwarai.

Kada mutum ya zama sai a sallah, Azumi, aikin Hajji kaɗai, yake Musulmi. Watau ya zama yana bin tsarin da ya saɓa wa na Allah. Allah (SWT) Yana cewa:

 “Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku shiga Musulunci gaba ɗaya (watau ku miƙa wuya gaba ɗaya). Kada ku bi takun sheɗan, ba na Allah ba). Shi abokin gaba ne a gare ku, bayyananne” (suratul Baƙarah, Aya ta: 208).

Abin takaici shi ne, a halin da muke ciki a yanzu, za mu ga cewa a dukkanin tsare-tsare nan na rayuwa babu wanda muke tafiyar da shi a kan tsarin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo da shi.

Misali: Tsarin Ilminmu ba ya  koya mana tauhid da tsoron Allah da ranar lahira da Tarbiyyar Musulunci. A tsarin zamantakewa.

Idan muka ɗauki zamantakewarmu ta aure da zaman iyali, ba a kan Alƙur’ani da sunnah take ba. Tsarin Tattalin arzikinmu cike yake da cin hanci da rashawa, cin riba, gululu, (Watau satar dukiyar jama’a) da sauransu.

Tsarin siyasarmu (shugabanci) tsari ne na Damakwaraɗiiyya, wanda babu Allah a  cikinsa.

Shi kuwa tsarinmu na shari’ah kowa ya san dokokin ‘yan Adam muke fifitawa a kan dokokin Allah (SWT). Abin nufi a nan shi ne, son Annabinmu  na baka ne kawai. Ba a aikace yake ba. Gashi kuwa Allah (SWT) yana cewa:

Gaya musu, idan ku kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah ya so ku, ya gafarta muku zunubanku. Allah mai gafara ne, mai rahama” (Suratu Ali Imrana, Aya ta:31)
Allah (SWT) yana cewa: Ka ce musu Idan iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan’uwanku  da matanku, da danginku da dukiyoyinku da kuka nema da hanyar samunku da kuke gudun kada ta yi tasgaro da gidajen da kuke jin daɗinsu, su suka fi soyuwa a  gare ku, maimakon Allah da Manzonsa, da  ƙoƙarin tabbatar da tsarinsa, to ku zauna, har sai Allah ya zo da lamarinsa (Mutuwa ko halakarwa). Allah ba ya shiryar da mutane fasiƙai”
(suratul Taubah, Aya ta:24).

Wannan duka yana nuna cewa ba za mu zama musulmi ba, sai mun gudanar da kowane ɓangare na rayuwarmu bisa tsarin Allah.

Wannan kuma ba zai samu ba, sai ta hanyar koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), watau ta hanyar riƙo da Alƙur’ani da Sunnah. Annabi(S.A.W) ya ce:

“Na bar muku nauyaya guda biyu, ba za ku ɓata ba, matuƙar kun yi riƙo da su: Littafin Allah da sunnata”

Domin sanin yadda sahabbai suke koyi da manzan Allah danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceYadda Sahabbai Suka Yi Koyi Da Annabi Muhammad (S.A.W)
Labarin na GabaYadda Ake Haɗa Lemon Tsamiya
Dr. Yahaya Tanko
A yanzu Dr. Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar Dukawuya FCE. A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki. Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.