Yadda Sahabbai Suka Yi Koyi Da Annabi Muhammad (S.A.W)

0
1001

Sahabban Annabi Muhammad (S.A.W) sun yi koyi da shi a cikin dukkanin harkokin rayuwarsu. Ba kawai sai a salla, zakka, Azumi da Hajji kaɗai ba. Ga wasu misalai ‘yan kaɗan da za su nuna mana haka.

Dab da Annabi Muhammad (S.A.W) zai yi wafati ya zartar da wata rundina ta yaƙi, ƙarƙashin shugabancin Usamatu bin Zaid. Bayan wafatin annabi Muhammad (S.A.W) sai wasu suke ganin ya kamata a dakatar da wannan runduna tukuna, kasancewar an sami wasu suna ƙin bayar da zakka. Har ma aka zama cikin tsoron kawo hari cikin Madina. Me Abubakar yayi a matsayinsa na shugaba? Abubakar bai yarda a dakatar da wannan runduna ba. Cewa ya yi:

“Ba za ta yiwu ba a gare ni, na kwance tutar da Manzon Allah (S.A.W) ya ƙulla”.

Haka nan sauran sahabbai suka goyi bayan Abubakar, Usamatu ya shugabanci wannan yaƙi kuma aka yi gagarumar nasara. Game da Madina kuwa, abin da Abubakar ya yi shi ne, sai ya sanya wasu daga cikin manyan sahabbai suka shugabanci wata runduna domin ba ta kariya, kamar su: Aliyyu bin Abi Ɗalib,
Zubairu binil Auwam, Sa’adu bin Abi Waƙƙas, Abdullahi bin Mas’ud da abdur Rahman bin Aufin.

Wani abin da Sayyidina Abubakar ya yi (na ruqo da tsarin Annabi) bayan wafatinsa (S.A.W), wanda yake nuna dagewarsa, shi da sauran sahabbai, a kan Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W) (watau tsarinsa na rayuwa) shi ne, wasu Larabawan ƙauye sun ƙi bayar da zakka bayan wafatin Annabi Muhammad (S.A.W). A wannan lokacin cewa ya yi:

“Wallahi! Idan da za su hana ni dabaibayi, wanda suka kawo wa Manzon Allah (S.A.W), da sai na yaƙe su”.

Wani abin da za mu sake lura da shi shi ne, yanayin da Nana faɗinmah ‘yar Manzon Allah (S.A.W) ta nemi gadon Annabi Muhammad (S.A.W), a nan ma sai y ace mata ya ji Manzon Allah ya ce:
“Mu jama’ar Annabawa ba a gadon mu. Abin da muka bari, sadaka ne”

(Bukhari da muslim ne suka ruwaito).

Wani misalin shi ne, wata rana Sayyidina Umar ya zo zai sumbaci  Hajarul Aswadi sai ya tsaya ya ce:

Ni na san kai dutse ne. Ba ka cutarwa, ba ka amfanarwa. In ba domin na ga  annabi  (S.A.W) yana sumbatar ka, da ba zan sumbace ka ba”.

(Bukhari ne ya ruwaito).

Wata rana Abdullahi bin mas’ud ya zo zai shiga masallaci sai ya ji Annabi Muhammad (S.A.W) yana
cewa:

“A zauna”. Sai ya zauna a kan dokin ƙofar masallaci. Bai ƙara yin gaba ba ko kaɗan, sabo da cika umarni.

Haka nan sahabbai suka yi ta koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), a dukkanin tsare-tsaren rayuwa. Wata rana Abdullahi bin Mugaffal ya ga wani mutum (ko wani ɗan ɗan’uwansa), yana yin jifan da ake kira ‘Hazfu (wadda akan sa tsakuwa a tsakanin babban ɗan yatsa da ɗan ali, a wulla ta). Sai ya ce da shi:

“Manzon Allah (S.A.W) ya hana yin hazfu. Da ya sake ganinsa yana yi sai ya ce:

“Ina gaya maka Manzon Allah (S.A.W) ya hana yin hazfu kana sake yi? Ba zan sake yin magana da kai ba, har abada

(Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).

Har ma ta kai cewa wasu daga cikin sahabbai suna koyi da Annabi, hatta a abubuwan da Annabi yakan y,i ba da nufin lallai sai an yi koyi da shi ba.

Abdullahi bin Umar ya shahara game da haka.

Abdullahi bin Umar ya kasance yana zuwa ƙarƙashin wata bishiya a Madina, ya yi baccin rana. Da aka tambaye shi game da haka, sai ya ce shi kawai ya ga Annabi yana yin baccin rana a ƙarƙashinta.

Wata rana Abdullahi bin Umar yana cikin tafiya tare da mutane, sai aka ga ya kewaye wani wuri, bai bi ta wurin ba, (Alhali babu komai a wurin), da aka tambaye, shi sai ya ce, ya ga Annabi wata rana suna tafiya ya kewaye wurin.

Haka nan wata rana an ga ya sauka a wani wuri tsakanin Makka da Madina, ya yi salla, dalilin sa shi ne, ya ga Annabi ya yi sallah a daidai wannan wurin suna halin tafiya. Duk da kasancewar a lokacin mutane sun yi masallaci a kusa da wurin, shi sai ya ƙi yin salla a masallacin, ya je ya yi a daidai inda Annabi ya yi (S.A.W)

Domin karanta cikekken littafin danna wannan koren rubutu

labarin da ya wuceMazajen Da Nana Khadija Ta Aura Kafin Manzon Allah (S.W.A)
Labarin na GabaYadda Za Mu Yi Koyi Da Annabi (S.A.W) A Dukkanin Tsare-tsaren Rayuwa
Dr. Yahaya Tanko
A yanzu Dr. Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar Dukawuya FCE. A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki. Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.