Falalar Yin Sadaka A Asirce

0
529

An karɓo daga Abu Harairata (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce: “Mutane bakwai Allah zai sanya su a cikin inuwarsa a yinin da babu wata inuwa sai inuwarsa:

1) Shugaba mai adalci.

2) Matashi da ya taso kan bautar Allah

3) Mutumin da zuciyarsa take a rataye a masallaci

4) Da mutanen da suke ƙaunar juna saboda Allah, suka haɗu a haka. Suka rabu a haka

5) Da mutumin da kyakkyawar mace mai matsayi ta neme shi, sai ya ce: Ni ina tsoron Allah

6) Da mutumin da ya yi sadaka a ɓoye ta yadda hagunsa ba ta san abinda damansa ta bayar ba.

7) Da mutumin da ya tuna Allah yana shi kaɗai, har ya yi ƙwalla. (Bukhari 1423, Muslim 1031).

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Dasa Bishiya
Labarin na GabaFalalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa