Yadda Wadatar Zuci Take

0
367

Wadatar zuci shi ne babban arziki wanda ba ya ƙarewa; wanda ya same shi, ya huce haushin da takaicin duniya, ba shi ba hassada ba ganin ƙyashi ba baƙin ciki ba ruwansa da ƙulle-ƙulle, ba ya tankwaɓarwa da wani arzikinsa.

Wanda yake da wadatar zuci ya huta; shi ne kaɗai yake jin daɗin rayuwarsa yake cin arzikinsa hankalinsa a kwance.

Wadatar zuci ita ce yarda da gamsuwa da jin daɗi da godiya ga Allah, a bisa abin da Allah ya ba ka na ni’imominsa; waɗanda ba su da iyaka misali: Rayuwa, lafiya, Sana’a, Mahalli, Iyali, abin hawa da sauran su, ba tare da hangen abin da wani ko wasu suke da shi ba, kuma ba tare da kwaɗayin abin kowa ba. Ita ake kira (Al- ƙaratu) da larabci.

Wato dai wadatar zuci ita ce kullum mutum ya dinga duban ni’imomin da Allah yai masa; yana jin daɗin su, yana duban na ƙasa da shi, yana godiya ga Allah yana gamsuwa da iya arzikinsa, ba ya hangen na wani ballantana ya sa rai ko ya miƙa hannun roƙo gare shi.

Mai wadatar zuci yana rayuwa cikin ‘yanci da mutunci da kuma rufin asiri; yana ji a ransa ko da an fi shi kuɗi ko muƙamai; to shi ma ya fi wani, koma ya fi sauran zama lafiya da kwanciyar hankali.

Domin karanta cikakken bayani a kan Fa’idojin Wadatar Zuci danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Bushewar Zuciya danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Litattafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; A kan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceFa’idojin Wadatar Zuci
Labarin na GabaHikimomi A Kan Wadatar Zuci