Da Ruhi Kake Mutum Ba Da Gangar Jiki Ba

0
926

Jiki kamar kayan aikin ruhi ne, wanda rai yake tuƙawa, ruhi shi ne haƙiƙanin ɗan Adam.

Ni’imar da ruhi ke ji, ta fi ta gangar jiki, kamar yadda ƙunar ruhi ta fi ƙunar jiki.

Ruhi ne yake jin zafi, amma ba irin na mintsini ko ƙonewa ba, irin na fushi, bakin ciki da damuwa,

Yakan ji daɗi amma ba irin na zaƙi ko garɗi ba, sai dai irin na farin ciki, bushasha da

annashuwa, kamar yadda yake da karfi irin na jarumta da dauriya,

Sabo da haka jin zuci ba irin jin gaɓoɓi ba ne, a irin wannan misalin, zuciyar mutum kamar ita ce wayoyin lantarkin sadarwa na ruhi.

Lalacewar zuciya da ƙwaƙwalwa ita ce lalacewar ɗan Adam gaba ɗayansa, domin zuciya

ita ce masaƙar labulen hali, na baɗini kuma mahaifar rayuwa ta zahiri.

Alakar ruhi, rai, zuciya da ƙwaƙwalwa ba abu ne mai wahalar fahimta ba, in mutum ya

auna da mafarki, kodayake wannan ba muhallin maganar mu ba ce, amma mu zurfafa nazari a kan faɗin Allah:

“Allah yakan ɗauke ruhi a lokacin da za su mutu, da kuma waɗanda ba su mutu ba, a barcinsu.

Sai ya riƙe shi daga waɗanda ya umarta wa mutuwa, sauran kuma sai ya dawo musu da shi a lokaci tabbatacce. Haƙiƙa a wannan lokaci, akwai alamu ga masu nazari” (Az-ZumarQ39:42).

14 Ita mutuwa hasara ce da ruhi ya yi na kayan aikinsa, a wannan duniya wato gangan jiki, kamar yadda mamaci ya yi hasara daga rabuwa da dukiyarsa, ‘ya’yansa, motoci da rigunansa, iyalai da mulkinsa.

Duk wannan hasaru ababe ne da mutum zai baƙin cikin hasarar su ta hanyar ruhinsa.

Kodayake ruhin masu ƙarfin imani, masana Allah, waɗanda zukatansu ke ta’allake da ruhin ubudiyyah hasken dake zuciyarsu kan mamaye gurbin adon duniya da dusashe wancan tunanin,

ta tabbatar masa da farin ciki a wannan sabon hali da zai shiga.

Duba:
Domin bayanai a kan Ruhi karanta littafin Ibnu Qayyim ‘Ar-Ruuh’

labarin da ya wuceYadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri
Labarin na GabaMe Yasa Ake Kiran Kakan Manzon Allah Da Suna Shaibah?