Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi

0
603

Idan aka yi la’akari da mutanen da za su amfana da waƙafi, ana iya kasa su kamar haka:

1. Ba da Waƙafi ga ‘Yan’uwa da makusanta, ba shakka addinin Musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa matuƙa a kan yin irin wannan nau’i na waƙafi, wato wanda mutum zai yi don taimakon ‘yan uwansa ta hanyar sadaukar da abin da wata dukiya tasa take samarwa gare su, kamar yadda Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kwaɗaitar da Abu Dalha a lokacin da ya sadaukar da gonarsa wacce ake kira Bairaha’ ana kiran irin wannan nau’i na waƙafi da sunan “alwaƙaf alahliy”.

2. Kuma Waƙafi na kowa da kowa don amfanin al’umma gaba ɗaya kamar yadda muka bayyana a baya cewa sayyidina Uthman bn Affan ya sadaukar da rijiya ga ɗaukacin al’umma, ana kiran irin wannan naui na waƙafi “alwaƙf alkhairiy al-alaam”.

3. Sannan bayar da Waƙafi ga wani nau’i na mutane: haka nan ya halatta a yi waƙafi ga waɗansu nau’i na mutane da aka ambata ko aka ambaci siffarsu kamar

wannan bayanin An ciro shi daga littafin Gudunmuwar Wakafi/ Hubusi Da Tasirin Wajen Gina Tallafin Arzikin Al’umma wanda Dr. Sunusi Iguda Kofar Nasarawa Da Shu’aibu Abdullahi Kafin Maiyaƙi Suka wallafa Domin karanta danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceGano Ciwo Shi Ne Makamar Sanin Maganinsa
Labarin na GabaMatakan Kula Da Tarbiyya Guda 100