A wannan matashiya, za a kawo taƙaitattun bayanai a kan mataki da hanyoyn tarbiyya da ya kamata iyaye su yi, ta hanyar karanta waɗannan bayanai, su kuma haɗa kai wajen aiwatar da su, domin samun zuri’a managarciya mai amfani ga kowa, zuri’ar da za ta samu lada mai ci gaba bayan mutuwar iyaye. Allah ka sa mu dace.
1.Tausayi da jinƙai
Ya kamata iyaye su kasance masu tausayi da Jin ƙai da bi sannu-sannu wajen tarbiyyar ‘ya’ya. Su yi koyi da Manzon Allah (S.A.W.) yadda yake tausaya wa ƙananan yara, yake jan su a jiki.
2. A guji zagi da tsinuwa
Waɗansu iyayen suka ɗauka gallazawa da tsanantawa da zagi da la’anta da ɗaure fuska shi ne kaɗai zai sa ɗa ya taso da tarbiyya. A gaskiya wannan kuskure ne babba.
3. A guji azabtarwa da yawan duka
Wannan ma kuskure ne ta yadda za ka ga waɗansu iyaye har hana ‘ya’yansu abinci suke yi, ko su yi musu zigidir su zane su, wannan yana da mummunan tasiri a fannin tarbiyya.
4. Koyarwa
Ya wajaba a rinƙa koyawa ‘ya’ya abinda zai amfane su da abin da zai cutar da su. A yi wannan koyarwar mataki-mataki gwargwadon shekaru da fahimtar yaro.
5.Wasiyyar Lukman (A.S)
Ya kamata a ɗora tarbiyyar ‘ya’ya kan wasiyyar Lukman (A.S) ga ɗansa wacce Allah Ta ala ya kawo ta a suratu
Lukman aya ta 12 19. Domin ta ƙunshi gaba ɗayan turakun tarbiyya. Yi ƙoƙari ku karanta waɗannan ayoyi tare da sanin ma’anoninsu.
6. Koyar da ladabi
Ladabi shi ne gishirin zaman duniya, wanda ba shi da ladabi komai ilminsa komai kuɗinsa komai mulkinsa ya yi asara. Lallai ne a koya wa ‘ya’ya ladabin zama da kowane irin rukuni na mutane, ladabi ga Allah da Manzonsa da Alƙur’ani da sauransu.
7. Tsoron Allah Ta’ala
A cusa wa yaro aƙidar tsoron Allah Ta’ala da yarda da cewa duk inda mutum yake Allah yana jin sa yana ganinsa yana sane da duk abinda yake aikatawa, babu abin da yake ɓuya a gare shi.
8. Imani da Alƙiyama
A dasa masa wannan a zuciyarsa, ya yarda cewa a wannan rana. Allah zai yi sakamako ga kowa kan abin da ya aikata na alheri da Aljanna ko na sharri da Wuta.
9. Ladabi ga Manzon Allah (S.A.W.)
A koya wa ‘ya’ya ladabi ga Manzon Allah (S.A.W.) ta yadda za su yi cikakken imani da shi, su rinƙa girmama shi, kada su yi masa kishiyoyi, su sallama masa, su ƙanƙame sunnarsa su tsani bidi’a, su guji munana ladabi a gare shi.
10. Ƙaunarsa da sahabbansa da iyalansa
A dasa ƙaunar Manzon Allah (S.A.W.) da sahabbansa da iyalansa (R.A) a zukatan ‘ya’ya ta yadda za su rinƙa koyi da su. Su guji aƙidar ƙin sahabbai da zagin su da allanta iyalan Annabi (S.A.W.)
11. Ladabi ga Al-ƙur’ani
Su yi imani da shi, su rinƙa ƙaunarsu., su haddace shi su san ma’anarsa, su rinƙa aiki da shi a kowanne ɓangare na rayuwarsu. Su ringa girmama shi ya zama shi ne jagoransu a rayuwa.
12. Bin lyaye
Lallai a koya musu biyayya ga iyayensu, musamman Uwa. Su ringa girmama su, su rinƙa yi musu godiya, da tausaya musu da taimakon su da kaucewa saɓa musu.
Yana daga ladabi ga iyaye sakaya sunayensu, Kada ɗa ya Jawo musu zagi, kada ya ɗaga muryarsa sama da ta su, ya yi magana da su cikin tausasawa da ganin girma.
14. Babu biyayya Cikin saɓon Allah.
A sanar da ‘ya’ya cewa babu wani mahaluƙi kowane ne shi da za a yi masa biyayya in ya yi umarni da saɓon Allah Ta’ala ko Manzonsa (S.A.W.).
15. A kyautata musu koda sun kauce hanya
Ƙin bin iyaye a kan saɓa wa Allah Ta’ala ba ya nufin a daina kyautata musu, a’a, a ci gaba da kyautata musu amma kada a yi musu biyayya a kan saɓon Allah Ta’ala. A koyar da ‘ya’ya wannan.
16. Koyi da Annabawa da Salihan bayi.
A nuna wa ‘ya’ya cewa a faɗin duniyar nan, babu waɗanda suka cancanci a yi koyi da su sai Annabwa da Sahabbansu da sauran bayin Allah nagari. Su guji kwaikwayon maƙiya Allah; maƙiya addinin Allah da Manzonsa.
17. Girmama Malamai
A koya musu girmama malamai da martaba su, kada su rinƙa kiransu da sunayensu, ballantana da sunan banza. Kada a rinƙa kushe malami a gabansu, a nuna musu cewa malami uba ne.
18. Umarni da Sallah
A tilasta su, su rinƙa yin sallah daga shekara bakwai, in sun shekara goma suka ƙi yin salla a doke su. Kafin su shekara bakwai a rinƙa lallaɓa su da kwaɗaitar da su a kan salla.
19. Alamomin Balaga
Tun kafin su balaga, ya wajaba iyaye da malamai su sanar da su alamomin balaga da sanar da su cewa, da zarar sun ga waɗannan alamomi, to, fa dokokin Allah sun hau kansu, kada su yi ta ɓarna ko su yi ta wasa da ihu suna jin cewa wai su yara ne.
20. Umarmi da kyakkyawa da hana mummunan aiki.
A sanar da ‘ya’ya kyawawan ayyuka da kishiyoyinsu, a koya musu hanyoyi umarni da kyawawan ayyuka a hana munana, bisa koyarwar Ƙur’ani da sunna da bin salon magabata na Ƙwarai.
21. Girmama manya da tausaya wa ƙanana
Iyaye su koya wa ‘ya’yansu su rinƙa yiwa duk wanda ya girme su kallon uba ko uwa, na ƙasa da su kuma, su ɗauke su a matsayin ƙanne. Su girmama manya su tausaya wa ƙanana, su yi kyakkyawar mu’amala da sa’o’insu a matsayin abokai.
22. Kula da kyawawan halaye
lyaye su ɗora ‘ya’yansu a kan halaye na haƙuri, juriya, wadatar zuci, nutsuwa, da mutunci su nisanta da munanan halaye, kamar girman kai, alfahari, wulaƙanci da sauransu.
23. Wasiyyar Manzon Allah (S.A.W.) ga Ibn Abbas
Lallai ne iyaye su tarbiyanci ‘ya’yansu a kan abubuwan da wasiyyar Manzon Allah (S.A.W.) ga Ibn Abbas ta ƙunsa.
Waɗannan abubuwa su ne: Bin dokokin Allah a kowanne hali, roƙon Allah da neman taimakonsa shi kaɗai, dogaro gare shi da rataya zuciya gare shi, shi kaɗai, sai ƙarfin hali da jajircewa da kyakkyawan fata a rayuwa.
Wannan hadisi shi ne hadisi na 26,669 a Musnad na Imam Ahmad na 2516 a Timizi na 19 a Arba’ una Hadis.
24. Wasiyyar ƙarfafa gwuiwa
Haka nan ya kamata a ɗora yara a kan wannan wasiyyar ta Manzon Allah (S.A.W.) wacce yake cewa: “Mumini mai ƙarfi ya fi alhairi, kuma Allah ya fi son sa fiye da mumini mara ƙarfi. Amma kowanne yana da alhairi. Ka dage kan abinda zai amfane ka, ka nemi taimakon Allah. Kada ka gaza, idan wani abu ya same ka, kada ka ce da na yi kaza da kaza ne zai faru. Kawai ka ce haka Allah ya ƙaddara, kuma abinda ya ƙaddara shi ne yake kasancewa, saboda irin waɗannan maganganu suna buɗe kofar shaiɗan.
25. Su guji kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe
A yi wa ‘ya’ya tarbiyyar nisantar kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe saboda suna kashe zukata, suna koya ɓarna suna buɗe ƙofofin sha’awa da fitintinu iri-iri.
26. Nisantar hotuna da gumaka
Asalin bautar gumaka ta faru ne daga kakkafa da liƙa hotunan bayın Allah, daga nan sai aka sassaka gumakansu, sai aka kama bauta musu. A yanzu abin jiya ya fara dawowa saboda haka a yi hattara. Hoto in dai ba na lalura ba ne, kada a yi sai dai hotunan abubuwa marasa rai ko waɗanda za a rinƙa tattaka su ana wulaƙanta su amma ba girmamawa ba.
27. Nisantar kafirci da danginsa
A dora ‘ya’ya a kan nisantar da ƙyamar kafirci da danginsa wato aiki na shirka da saɓo irinsu zage-zage da shaye-shaye, maganganun batsa, caca, karance-karancen batsa da soyayya, tsafi da camfe-camfe da sauransu.
28. Yaba wa yaro in ya yi abin kirki.
Yana daga hanyoyin tarbiyya, a yaba wa yaro in ya yı abin kirki, a yi masa addu’a, amma kuma kada a yi masa yabon da zai sa masa girman kai, ko kuma duk lokacin da ya yi kirki ya saurari yabo, ta yadda kuma zai koma yin abu ba don Allah ba, sai don a yaba masa.
29. Salla da addu’ar Istihara
Tun da wurwuri a koya wa yara yadda ake yin istihara don su kaucewa istihara ta bidi’a da bokanci. Saboda Manzon Allah (S.A. W.) yana koyar da istihara kamar yadda yake koyar da karatun Ƙur’ani.
30. Ba da kyauta
Ba da kyauta ko wata shaida ta yabo kan kula da sallah ko ƙoƙari a makaranta da sauransu abu ne mai kyau a fannin tarbiyya. ldan wani ya yi ƙoƙari an ba shi kyauta to shi kuma wanda bai yi ƙoƙarin ba, sai a dubi wani ɓangaren da ya yi koƙari a kansa kamar tsafta ko kula da salla a yi masa kyauta a kan wannan.
31. Yin faɗa da nasiha a ɓoye
Idan yaro ya yi laifi, kada a yi masa faɗa ko nasiha a gaban ‘yan uwansa, a’a ya kamata a yi masa a keɓance musamman in abin da ya yi ba halinsa ba ne, ko kuma ya yi ne a ɓoye.
32. Ya san dalilin horo
Hanyoyin horo suna da yawa sun haɗa da: ɗaure fuska, ƙin yi masa magana, hana shi abin wasa, ko yin wasan, ba shi hadda ko wani rubutu da sauransu, ba duka ne kawai hanyar horo ba. Kuma ya san dalilin da ya sa aka yi masa horon.
34. Horo da duka
Ba a yin horo da duka, sai bayan an yi gargaɗi, an bi dukkannin hanyoyin da suka gabata, ba su yi amfani ba. Kuma ya san dalilin dukan, kada kuma a yi duka a fuska da maƙarfafa, kada a haɗa da zagi ko wani abu na wulaƙanci, kuma dukan ya kasance sama-sama.
35. Adadin bulala
Ba a dukan yaro a kan barin haƙƙin Allah Ta’ala, sai ya kai shekara goma, kuma ba a wuce bulala goma tare da sharaɗan da suka gabata.
36. Ku kasance abin koyi ga ‘ya’yanku
Mai dokar barci bai kamata ya yi gyangyaɗi ba. Saboda haka ya wajaba iyaye da malamai da dukkanin manya, su kasance managarta domin yara da su suke koyi. Kada a rinƙa faɗa ba aiki, ko aiki ya rinƙa saɓawa magana.
37. Haɗin Kai
Ya kamata uwa da uba bakinsu ya zo ɗaya a kan tarbiyya, kada su raba hankalin ɗa wannan ya ce yi, wannan ta ce kada ka yi, wannan yana da hatsari babba.
38. Lallai ne uwa da uba su ɓoye duk wani saɓani da yake a tsakaninsu, ta yadda ‘ya’yansu ba za su fahimci me ake yi ba. Kada su yi ko da musu a gabansu ballantana dambe da zage-zage.
39. Sai fa an haɗa da naci
Tarbiyya a wannan zamanı tana bukatar naci da haƙuri da yawan maimaitawa da bibiya, saboda yawaitar masu rusa tarbiyya da matsanancin naci da maimaita ɓarna da suke yi ba dare ba rana da hanyoyi da salo daban-daban.
40. Yanayi mai kyau
Ya kamata a samar da yanayi mai kyau na tarbiyya, wannan yanayi ya haɗa da auren mace/miji managarci/managarciya da samun maƙota da abokai da malamai managarta. In waɗannan suka haɗu, tabbas za a samu tarbiyya insha Allah.
41. Abokai da malamai nagari
Ya kamata iyaye su taimaka wa ‘ya’yansu wajen zaɓa musu abokai da ƙawaye da malamai nagari. Saboda zama tare yana da tasiri ƙwarai da gaske wurin kwaikwayo da nason hali.
42. A raba su da muggan abokai da ƙawaye
Ya wajaba su hana ‘ya’yansu yin abota da lalatattun abokai da ƙawaye cikin hikima da dabara, ba tare da nuna musu cewa su tsarkakakku ba ne. Waɗancan kuma wasu najasa ne.
43. Kada ku yi nesa da ‘ya’yanku
Ya kamata duk inda ‘ya’ya za su je, ya kasance da sanin iyayensu. lyaye mata su rinƙa zama da ‘ya’ya mata, su kuma maza ya kamata su rinƙa tafiya da ‘ya’ya maza wurin ayyukan alhairi, Saboda su saba, kuma su rinƙa koyar kyawawan halayensu.
44. Siffofin malamai
A nutsu sosai wurin zaɓar malaman da za su koyar da ‘ya’yan, su kasance masu mutumci da hankali da ladabi da ilhami, da riƙo da addini da hikima da tsafta da tausasawa.
45. Malamai su haɗa kansu
Malamai a matsayinsu na ginshiƙi a fagen tarbiyya, ya kamata su haɗa kansu, kada wani yana tufka wani yana warwarewa. Kada malamin wani fannin ya raina na wani fannin.
46. Son ya zo na ɗaya a kowane fanni
Ya kamata malamai da iyaye su dasa wa ‘ya’ya son da ƙaunar gasa da juna wajen zama na ɗaya a kowane fanni na rayuwa. Kada su taso da aƙidar “da ƙyar na sha, ya fi da ƙyar aka kama ni” a’a kada ma a ce an biyo ka da gudun tuni ka yi gaba shi ya fi.
47. Karatu a gida
Lallai ne duk runtsi da kujiba-kujiba a ware lokaci a gida da za a rinƙa karatu na gaba ɗaya, a maida hankali wajen karatun hadisin kwaɗaitarwa da tsoratarwa da fiƙhu da tafsiri da sira da Arabiyya.
48. Ɗabi’ar Karatu
Ya kamata iyaye su koya wa ‘ya’yansu ɗabi’ar yawan karance-karance da son karatu da tara littattafai, kada a bar su, su yi wa komfuta matsanancin sabon da za ta sa su ƙauracewa karatu da littafi.
49. A samar da laburare
Samar da daƙin karatu in da hali a gida, ko yin wasu ‘yan kantoci da jera littattafai a cikinsu da ake karantawa, zai taimaka wajen cusawa ‘ya’ya ɗabi’ar son karance-karance.
50. Kwana a gidan ‘yan uwa
Ba da dama ga ‘ya’ya su rinƙa ziyartar gidajen danginka, kai har ma su kwana in ta kama, wannan abu ne da yake koya wa ‘ya’ya zama da mutane da mu’amala da su da sabo da rashin abin da aka saba da shi
51. Shiga Cikin Jama’a
Kada a ƙuntata wa yaro a cukwikwiye shi a gida, ba ya zuwa ko’ina, ba ya hulɗa da kowa daga makaranta sai gida, a rinƙa ba shi damar shiga cikin jama’a da halartar sabgogi da suka dace da shari’a da shekarunsa, a bisa kulawa da sa idon iyaye da ‘yan uwa.
52. Yin raha da yara
Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai sakin fuska yakan yi raha da kakaci, har da ƙananan yara. Saboda haka lokaci zuwa lokaci iyaye su rinƙa yin raha da ‘yan wasanni da ‘ya’yansu waɗanda suka dace da shekarun kowannensu.
53. A Koya musu siye da siyarwa
Ya kamata iyaye su koya wa ‘ya’yansu wayewar saye da sayarwa, gwargwadon shekarunsu. Kada a bari har su girma ko ƙirga ba su iya ba, ko ma ba sa iya bambamcewa tsakanin takardun kudi, ballantana saye da sayarwa.
54. Riƙe sirrin gida.
A koya wa ‘ya’ya riƙe sirrin gidansu da sauran abubuwan da suka shafi iyali, kada a bari yawan surutunsu ya kai matsayin da har zai je waje yana yaɗa sirrin gidansu.
55. Kada ya rinƙa faɗar matsalolinsa
A sanar da ‘ya’ya cewa bai kamata su rinƙa fadar matsalolin da suke ciki ba, sai ga wanda yake ganin zai iya ba shi mafitar warware wannan matsalar, kamar iyaye da malamai.
56. Daidaita kishi da gasa
Dukkan ɗan Adam yana da ɗabi’ar ƙananan yara, wannan ne yasa yaya yake kishi da ƙanınsa. Jariri shi ma yana son a rinƙa ɗaukarsa da sauran kulawa kamar a da, to a nan iyaye su saita wanan ɗabi’a cikin hikima, kamar a ɗauke hankalinsa da wani abin wasa. A juyar da ɗabi’ar gasa wurin karatu da sauran ayyukan alhairi.
57. Addu’a
Kada iyaye su gaza ko su ƙosa wajen yi wa ‘ya’ya addu’ar neman shiriya da nagarta. A rinƙa bibiyar lokutan amsa addu’a, a rinƙa yawaita sadaka da kyautata wa malamai da mabuƙata a kan wannan manufa.
58. Ban da baƙar Addu’a
Duk ɓacin ran da iyaye za su shiga, su iya bakinsu, kada su kuskura su yi wa ‘ya’yansu baƙar addu’a ko baki. Wannan abu ne mai hatsarin gaske a kan dukkan al’umma.
59. Bayar da tsaro
Ya wajaba iyaye su kula sosai da tsaron lafiya da hankali da mutumcin ‘ya’yansu. Su daina sakinsu kamar dabbobi, musamman farkon dare lokacin da shaiɗanu suke fara dabdalarsu.
60. Hana kwanciyar rub da ciki
Manzon Allah (S.A.W.) ya ga wani ya kwanta rub-da-ciki sai ya ce: “Wannan kwanciyar Allah ba ya son ta (Abu Dawud, Timuizi, Ahmad). Kuma likitoci sun tabbatar da cewa wannan kwanciyar cike take da illoli da jawo cututtuka.
61. Nisantar da motsa sha’awa
A kula da abubuwa masu motsa sha’awa a rinƙa nesanta yara daga gare su, kamar kwanciyarsu a mayafi guda, cuɗanyar maza da mata, bayyana tsiraici, kalle-kalle da karance-karancen soyayya da batsa.
62. Kau da kai daga kallon tsiraici
A tarbiyyar yara a kan runtse idanu kan kallon mata da tsiraici ta hanayar karantawa da nisantar na’urori masu yaɗa hotuna da fina-finan batsa.
63. Koya wa mata suratun Nur
Suratun Nur ta ƙunshi hukunce-hukuncen hijabi da neman izini da sauransu, saboda haka Sayyadina Umar yake ba da umarni ga wakilansa su rinƙa koya wa mata wannan sura tare da bayanin ma’anoninta.
64. Su nisanci lalata.
Tun da wuri a sanar da yara haramcin zina luwaɗi da Maɗigo ta hanyar da ta dace da fahimtarsu da shekarunsu.
65. Kare mutunci da matsayi
A cusa wa yara kishin kare mutuncinsu da matsayinsu. A koya musu cewa duk abinda ba ka so a yi maka, to kada ka yi wa wani. Ka tsare mutuncin mutane, sai a tsare maka naka.
66. Kunya
Kunya tana daga cikin imani, a koya wa yara ɗabi’ar jin kunya, bayyana tsiraici da sanya matsattsun kaya masu bayyana tsiraici da jin kunyar saɓa wa Allah, da shiga haƙƙin mutane.
67. Daga shekara Bakwai
Tarbiyyar suturce jiki da sanya cikakken hijabi ga mata ya kamata ya fara tun daga shekara bakwai na rayuwar ‘ya’ya.
68. Idan ta balaga
A yayin da yarinya ta balaga ta hanyar fara al’ada ya wajaba ta rinƙa rufe gaba ɗayan jikinta kafin ta fita, ko a lokacin da take tare da wanda ba muharraminta ba.
69.Kowa ya sanya kaya irin nasa
Lallai ne iyaye su kula da suturun ‘ya’yansu, maza su sa kayan maza, mata su sa kayan mata.
70. Ban da kwaikwayon kafirai da fajirai
Kada iyaye su ƙyale ‘ya’yansu suna kwaikwayon suturu da ɗabi’u na kafirai da watsattsun mutane irin waɗanda ake ganinsu a kafafen sadarwa da sauransu.
71. Auren Wuri
Ya kamata iyaye su taimaka wa ‘ya’yansu maza su yi aure da wuri, muddin sun samu sana’a da nutsuwa da ilmi, daidai gwargwado, Kada a ƙyale su har su ƙosa ba aure, saboda babu abinda zai magance yawaitar lalata sai aure.
72. Daƙile aƙidar tsarin iyali
Tsarin iyali wani abu ne da yanzu yake nema ya zama kamar wani abin yayi. Wannan tsarin yana da illoli masu yawa na kusa da na nesa. A koyar da matasa masu aure da masu shirin yin aure illolin tsarin iyali. A koyar da su hanyoyin faɗaɗa sana’o’i da inganta su da kuma tarbiyyar wadatar zuci.
73. Tarbiyyar sha’awa
Addinin Musulunci ya koya yadda ɗan Adam zai sarrafa sha’awarsa ya bayyana halal da haram da hanyoyin riga kafin aikata laifuffukan jinsi, ya wajaba ‘ya’ya su san wannan tsarin da hukunce-hukuncen tun kafin balagarsu.
74. A rinƙa yin kinaya
Dukkan bayanar da koyarwa da suka shafi alaƙar mace da namiji da maganar Jinsi ya wajaba su kasance cikin tsafta da amfani da kalmomi masu tsafta ban da gatsal-gatsal don gudun gyaran gangar Auzunawa.
75. Neman lzini
A koya wa ‘ya’ya hukunce-hukuncen neman izini da sallama kafin shiga gida ko ɗaki. Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da amfani.
76. Hulɗa da mutane
Ya kamata a koyar da ‘ya’ya yadda ake hulɗa da kowane jinsi na mutane misali malamai iyaye, maƙota, shugabanni, ‘yan uwa, tsofaffi, masu buƙata ta musamman da sauransu.
77. Shawara da su
Yin shawara da ‘ya’ya musamman a kan abin da ya shafe su, da kuma harkar gida a lokacin da ya dace, abu ne mai kyau ƙwarai da gaske a fannin tarbiyya.
78. Tashen balaga
Wannan lokaci ne mai muhimmanci da rikice-rikice a rayuwar ‘ya’ya. Yana farawa daga shekaru goma sha uku zuwa shekaru goma sha takwas. Ya wajaba iyaye su fahimci haƙiƙanin yadda wannan mataki yake da buƙatun yara a wannan lokaci da yadda ya kamata a ɓullowa matsalolin lokaci.
79. Hira da ‘ya’ya
Ya wajaba iyaye su rinƙa zama suna yin hira da ‘ya’yansu, a irin waɗanan lokuta ne, za su rinƙa koya musu ladaban hira da tattaunawa, da ma ilmin zaman duniya.
80. Yawan Tambayoyi
Kada iyaye su nuna ƙosawa ga yawan tambayoyi na ‘ya’yansu, kada su rinƙa kwaɓar su a kan irin waɗannan tambayoyin. A ba su amsa gwargwadon hankalınsu. In tambayar ta fi ƙarfinka sai ka waske ta hanyar dabara.
81. Sauraron ‘ya’ya
ldan yaro ya zo maka da matsala, ko ya kawo maka ƙara ka tsaya ka saurare shi komai rashin muhimmancın matsalar, shi a wajensa muhimmiya ce. da haka zai saba har ya rinƙa kawo maka muhimman matsalolin. kuma ya koyi ɗabi’ar sauraron mutane da taimakonsu.
82. Girmama yara
Kada a rinƙa walaƙanta yara da nuna musu su kamar su ba mutane ba ne. wasu iyayen har ɗa ya yi furfura yana nan a matsayin yaro a wurinsu. Wannan babban kuskure ne.
83. Adalci
Ya wajaba iyaye su yi adalci tsakanin ‘ya’yansu maza da mata, manya da ƙanana. ‘ya’yan uwargida da ‘ya’yan amarya. Wannan yana taimakawa sosai a fannin tarbiyya.
84. Ciyarwa Ibada ce
Ya kamata iyaye su sani cewa, ciyar da iyali da kula da ɗawainiyarsu ta lafiyarsu ilminsu da sauransu ibada ce. Saboda haka su saki ransu su yi farin ciki, ban da yi wa ‘ya’ya gori ko gaya musu maganganu da suke nuna ƙosawa ko jin haushin ɗawainiyar da yake yi.
85. Banda shagwaɓawa
Kada iyaye su shagwaɓa ‘ya’yansu, a ƙarshe sai su zo su fi ƙarfinsu, su gagari kowa.
86. Kwanciyar hankali
Duk wani abin da zai firgita yaro, ya tayar masa da hankali ya kamata a nisanta razana, yana da mummunan tasiri a kan tarbiyyar ‘ya’ ya.
87. Tarbiyar ‘ya’yan fari
Lallai iyaye su kula sosai da tarbiyyar ‘ya’yansu na fari. Kada ɗoki da soyayya ta sa a bar su su sangarce. ldan na farkon suka gyara, to haka ‘yan gidan za su taso, in kuwa suka karkace, to haka abin zai ta tafiya. Wannan kuma ba ya nufin daga kun manyanta a dakata ba, a’a, a ci gaba harkan ɗan auta.
88. Tarbiyyar ‘ya’ya mata
A kula sosai da tarbiyyar ‘ya’ya mata, saboda su ne masu raino da kula da ‘ya’ya fiye da iyaye maza. In mata suka samu tarbiyya, duk al’umma za ta gyaru.
89. A kula da marayu
Lallai ne al’umma su kula da marayu a ba su ingantacciyar tarbiyya saboda maraici zai iya samun ‘ya’yan kowa kuma ba a san irin amfanin da marayun nan za su yi ba ga al’umma in sun sami tarbiyya mai kyau.
90. Kalmar farko
A yi ƙoƙari kalmar farko da yaro zai buɗi baki da ita ta kansance Laa ilaha illallahu.
91. Girmama baƙi
A koya wa ‘ya’ya girmama baƙi da yi musu hidima. Kada kuma su zauna, su zura idanu su buɗe kunnuwa suna jin hirar da ake yi.
92. Haƙƙokin hanya
Hanya tana da haƙƙokin waɗanda suka haɗa da tafiya cikin nutsuwa, da bin dokokin tuƙi tsaftace hanya, kada a ci wani abu a wurgar, da leda ko ɓawo a kan hanya. A kawar da abu mai cutarwa, kada a yi fitsarı ko kashi a kan hanya da sauransu. A koya wa yaro waɗannan ladabai.
93. Lokacin Hutu
A yi amfani da lokutan hutun ‘ya’ya wajen shirya musu abubuwa masu amfanı kamar tafiye-tafiye da wasanni masu ma’ana da koyon sana’o’i da karatuttuka na musamman.
94. Wakilci
Idan yaro ya ɗan data, a rinka wakilta shi a kan waɗansu abubuwa da suka dace don ya taso da tarbiyyar hulɗa da mutane.
95. Cika alƙawari da gaskiya
Kada ka yi wa ɗanka alƙawarin da ka san ba za ka iya ba. Duk abin da za ka faɗa wa ‘ya’yanka ka tabbatar gaskiya ne. kada ka rinƙa shara ta, sai girmanka ya faɗi, kuma su ma su zama maƙaryata.
96. Rarraba ayyuka
Ka raba wa ‘ya’yanka ayyuka, kowa ka dubi abin da ya fi dacewa da shi saboda gida kamar masarauta ce, akwai buƙatar sarki, waziri, fadawa (masu ba da tsaro) da sauransu.
97. Neman afuwa
Ku koya wa ‘ya’yanku ɗabi’ar yarda da amsa kuskure in sun yi da kuma neman afuwa. Su ga misali daga gare ku.
98. Fasaha
A lokacin da yaro ya yi wani kuskure na magana, ko ya yi shirme, ka gyara masa don ya taso da hikima da fasaha.
99. Kowa da irin baiwarsa
Ya kamata iyaye su kula da bambance-bambancen da suke a tsakanin ‘ya’yansu da irin baiwar da Allah ya yi wa kowane ɗaya daga cikinsu. Sai a sarrafa wannan baiwar da Allah ya yi wa Kowane ɗaya daga cikinsu ta yadda za amfani kansa da al’umarsa.
100. Tsoron Allah
Babban al’amari mafi muhimmanci a komai, shi ne tsoron Allah a fili da ɓoye da neman ilimi da aiki da shi, Ya Allah ka ba mu zuri’a managarciya.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Mansur Dala ya wallafa shi, domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.