Kun ga wannan abin? A yi hattara da cinsa kar ya zama abin ci akai-akai ballantana kuma kullum-kullum.
Ba kashewa masu sana’ar sa kasuwa nake ba, sai dai gaskiya duk wani smoked fish (bandar kifi ko wanne iri ne) yana da hatsari me girman gaske. In za a ci ya zamto jefi-jefi.
Yana ƙunshe da (carcinogens) wanda ke kai mutum ga samun cutar sankarar babban hanji haɗe zuwa dubura wato (Colorectal Cancer) wacce tana daga cikin cuttukan cancer biyar da ke kisa ba ji ba gani yanzu a Najeriya.
Sai dai wani karatun mutane ba za su fahimta yanzu ba domin matsalar ba take ne za ta bayyana ba, wani abin zai jira ka ne sai ka je daidai wasu shekaru ciwon ya bayyana alhalin ka mance ma kai gangancin a baya, wani lokacin kuma ya bayyana da wuri amma ka yi ta yawon asibiti ana ba a gane me ke damunka ba, a yi ta batun typhoid, cholera, ulcer da sauransu domin ana zaton colorectal cancer ba abu ne common game shekaru irin naka ba, sai a ƙarshe sanda aka yi gwajin da ya dace a gano matsalar, sannan wataƙil tama yaɗu ta shafi hanta da huhu ko ƙwaƙwalwa ka ga ka gama yawo, cancer wajen uku ce jikinka sai dai a janjaɓa amma an san ba makawa tafiya ce ta matso.
Domin karanta bayani akan Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure) Danna nan
[…] Yana dakyau kuranta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi) […]