Abubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

0
334

Akwai abubuwa da dama waɗanda suke kawo tabbataccen da dauwamammen zaman lafiya da tabbataccen kwanciyar hankali ga ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi, kai har da duniya ma gaba ɗaya.

Amma duk waɗannan abubuwa in aka dunƙule za su iya zama abu ɗaya tak, shi ne imani da bin dokokin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Wannan shi ne zai yi wa mutum jagoranci domin samun nutsuwa da hutun zuciya maras misalı, kuma ya zauna da kowa lafiya ta hanyar bai wa kowa haƙƙinsa.

Ga kaɗan daga cikin waɗannan abubuwa:

1. Imani da aiki nagari

Allah Ta’ala ya ce: Duk wanda ya aikata aiki nagari, namiji ne ko mace, kuma yana mai imanı, to za mu raya shi rayuwa mai daɗi. (Suratun Nahl: 97). Kuma Allah yana cewa: “Waɗanda suka yi imani da Allah da ranar lahira, babu tsoro a kansu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba” (Sura Mai’da” 69).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce, “Lamarin mumini yana da ban mamaki, komai nasa alhairi ne, in ban da mumini babu mai samun haka. Idan alheri ya same shi, sai ya gode wa Allah, sai ya zama alhairi, in kuma sharri ya same shi, sai ya yi haƙuri, wannan sai ya kasance alhairi a gare shi” (Muslim 18/125).

Wannan hadisi yana nufin in dai akwai Imani a zuciyar mutum, to babu wani abu a duniyar nan da zai dagula masa lissafi, ya hana shi sakat, ballantana ya tayar masa da hankali.

Mu ɗauki misalin wani mumini guda ɗaya, shi ne Shaihul Islam Ibn Taimiyya. Wannan bawan Allah ya shiga tasku iri-iri, ya sha ɗauri da duka da korar kare daga garinsu, laifinsa kawai shi ne, dagewa da matsanancin naci kan gaskiya, kai a ƙarshe dai a kurkuku ya mutu. A dab da mutuwarsa, yake faɗa a cikin kurkukun Dimashƙa: “Babu fa yadda maƙiyana za su yi da ni, ni aljannata da lambuna yana cikin zuciyata, duk inda na je, ina tare da ita ba na rabuwa da ita, ɗaure ni, halwa ce, kashe ni shahada, in kuma an kore ni, na samu damar yawata duniya domin nazarin ayoyin Allah da ikonsa.

Allahu Akbar! Allah ya jiƙan maza, maza sun faɗi.

2. Imani da ƙaddara

Ya ɗan’ uwa mai karatu, in kana fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka yarda da cewa duk abin da ya faru a duniyar nan, gare ka ko ga waninka, mai daɗi, ko marar daɗi, to haka Allah ya nufa, haka ya so, haka ya ƙaddara, kuma in duk duniyar nan za ta haɗu a kan a canja wannan abu, ba zai yiwu ba. To in ka yarda da haka, sai ka huta wa zuciyarka, ka sami nutsuwa.

Ga wani misali mai ƙayatarwa, ciwon daji ya fito a ƙafar Urwatu Ibnuz Zubair (Radiyallahu Anhu ) sai Likitoci suka ce za su ba shi giya ta bugar da shi, domin a guntule ƙafar cikin sauƙi. Sai ya ce atafau ba zai yarda ya sha giya ba ta kowane hali. Sai ya ce, “In so kuke sai lokacin da hankali na ya gushe za ku guntule min ƙafa, to ku bari sai na fara sallah”.

Hakan kuwa aka yi, yana sallah aka guntule ƙafar, bai ko motsa ba, sai da aka tsoma dungulmin cikin tafasasshen mai, sai ya suma. Can cikin dare sai ya farka, ya ji ana yi masa jajen kafarsa da kuma ta’aziyyar mutuwar ɗansa a wannan ranar! Amma saboda tsabar imani sai ya ce “Alhamdu lillahi tun da Allah ya ba ni lafiya kuma ya bar mun ɗaya ƙafar da ragowar ‘ya’yan.

Allahu Akbar! ka ji salaf na gaskiya, to yanzu wane abu ne zai iya tayar da hankalin wannan bawan Allah?

3. Ilmin Addini

Ilmi shi ne gishirn rayuwa, shi ne fitila mai kau da duhun jahilci da talauci da ɓacin rai da duk wata damuwa. Mai ilmi yana cikin farin ciki da daɗin da ba wanda zai iya siffanta shi, sai wanda ya shige shi, saboda babu tsoron kowa a zuciyarsa, sai na Allah.

An yi wani azzalumin sarki a Masar mai suna Ahmad Ibn Tuluna, wanda aka ce ya kashe sama da mutum dubu goma sha takwas (18,000) ta hanyar hana su ci da sha, har sai sun mutu.

Kowa yana tsoron wannan mamuguncin sarki, amma wani malami mai suna Abul Hasan Zahid (Radiyallahu Anhu) ya yi ta maza, ya yi shahada ya fuskance shi, ya je ya yi masa wa’azi kan irin ta’asar da yake aikatawa. Ai fa nan da nan ya harzuƙa, ya kufulo, ya sa aka damƙe wannan malami aka jefa a kurkuku. Ya sa aka kamo zaki, aka hana shi abinci kwana uku, sannan aka tura shi ɗakin da malam yake.

Wayyo! Ɗan uwa me kake zato zai faru? Ai malam ko a jikinsa, yana zaune ya fuskanci alƙibla, ya Sunkuyar da kansa kamar mai tunani. Shi kuwa zaki sai ya yi ta kewaya malam yana kaɗa jela kamar kare ya ga uban gidansa. Da ya gaji sai ya fito ya kama gabansa.

Wannan abu ya bai wa kowa mamaki musamman wannan azzalumi (Ɗan Tuluna), waje ya ruɗe da kabbara da godiya ga Allah, saboda kuɓutar malam Abul Hasan. Shi da kansa Sarki ya zo ya ba shi haƙuri, ya ce, “Don Allah wai tunanin me kake yi lokacin da zakin nan ya yiwo kanka, na ga kai ko damuwa da shi ba ka yi ba?

Sai ya ce, “Ai ni a lokacin tunanin hukuncin miyan zaki nake yi idan ya taɓa ni, shin najasa ne ko tsarkakakke? Sannan ya ce to ba ka ji tsoron zakin ba? Sai ya ce sam Allah ya yaye min wan nan. Kai ɗan uwa in ka na son jin daɗi na gaskiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali to ka nemi ilimin addini saboda Allah kuma ka yi ƙoƙarin aiki da shi. Allah ya sa mu dace.

4. Yawan ambaton Allah da karatun Ƙur’ani

Allah Ta’ala ya ce: “Ku faɗaka da ambaton Allah ne zukatu suke nutsuwa (Suratur Ra’adi:28).
Duk mutumin da yake yawaita zikiri, zai rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wanda kuwa bai damu da zikirin ba, ya shiga uku.

Allah Ta’ala ya ce: “Wanda ya kau da kai daga ambaton Allah, za mu hore masa wani shaiɗani ya kasance tare da shi (Suratu Zukhruf: 86). Kuma ya ce: “Duk wanda ya kau da kai daga Ambato na, to haƙiƙa rayuwar ƙunci za ta tabbata a gare shi, kuma za mu tashe shi ranar ƙiyama makaho (Surat Taha: 124).

Kuma Allah ya ce: “Bone (azaba, wahala, tashin hankali) ya tabbata ga masu busasshiyar zuciya daga ambaton Allah, waɗannan suna cikin ɓata bayyanan ne” (Surat Zumar:22).

Waɗannan ayoyın suna nunı ga tasirin da zikiri ya ke da shi wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma ya kamata ka sani cewa, zikiri kala-kala ne, wannan ya haɗa da karatun Ƙur’ ani da hadisi da ilmin Musulunci da addu’o’in ma’aiki, tun daga wayewar garı, har kwanciya barci, tunani kan ikon Allah da hikimominsa, tuna Allah lokacin aikata alhairi ko sharri, hailala, tasbihi, istigfari salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da sauransu.

Sannan ka sani cewa zikiri da duk wata ibada ba za su yi amfani ba, sai an yi su saboda Allah kuma daidai da yadda Allah da Manzonsa suka yi umarni, babu ƙari, babu ragi. Allah ya ganar da mu.

5. Sakin rai

Ya ɗan’uwa, in kana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka saki ranka ka tsarkake Zuciyarka daga duk wani dagwalo da tsatsa, waɗanda suke tayar da hankali irinsu hassada da girman kai da gaba da ganin ƙyashi da riya da jiji da kai da sauransu.

6. Kyautata wa mutane

Kyautata wa mutane ta hanyar nuna musu ƙauna da fatan alheri, da taimakonsu, da ba wa kowa haƙƙinsa, da girmama su, yana da tasiri mai ban mamaki wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Mutum mai alhairi yakan samu karɓuwa da farin jini a cikin al’umma, kai yakan fi waɗanda ya kyautatawa jin daɗi da farin ciki. Wannan abu an gwada an gani, yi ƙoƙari ka shiga cikin ayarin masu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

7. Ka hangi na ƙasa da kai, ka daina hangen na sama da kai

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Ku rinƙa duban na ƙasa da ku, ku dai na hangen na sama da ku, saboda kada ku raina baiwar Allah a gare ku”. (Muslim ne ya rawaitoshi).

Wannan Hadisi ya shimfiɗa ƙa’idar zaman lafiya da kwanciyar hankali, wato a kullum kada ka raina baiwar da Allah ya yi maka, duk halin da kake ciki ko mai muminsa, in ka duba ƙasa za ka ga ka fi waɗansu da dama, ka ga sai ka ji daɗi ka gode wa Allah, hankalinka ya kwanta. Amma idan kana hangen waɗanda suka fi ka, to ka shiga cikin taskar wahala da tashin hankali ke nan.

Sai dai kuma wannan ya shafi abin duniya ne kawai, amma a harkar ilmi da addini, so ake yi kullum ka rinƙa hangen na sama da kai, domin ka yi himma ka yi koyi da su. In kuwa kana duban na ƙasa da kai a ilimi da ibada, sai lalaci da girman kai ya kama ka, shi ke nan kuma sai komai ya ruguje.

8. Gajarta buri

Ka sani cewa rayuwar nan ta duniya taƙaitacciya ce, saboda haka, kada ka sake ka taƙaice ta da yawan tunane-tunane da damuwa kan abin da bai zo ba ko kuma wandą ya riga ya wuce. Ka sani cewa rana da wata ba za su tsaya jiran ka ba, yi ƙoƙari ka amfani lokacinka da ayyukan alhairi, kada ka rinƙa dogon buri.

Wata rana waɗansu mutane masu tsoron Allah suna tattaunawa kan gajarta buri. Sai ɗaya ya ce: “Ni a yanzu in na kai loma ɗaya bakina, ba na sa ran zan sake kai ta biyu” . Ɗayan kuwa sai ya ce, “Cafɗi-jan! Kai kana da ɗauka da yawa. Ai ni duk yayin da na ja numfashi ba na sa ran zan sake jan wani!” Allah Akbar, ɗan uwa duk wanda bai ɗauki duniyar nan da zafi ba, to haƙiƙa shi ne cikakken mai zaman lafiya da kwanciyar hankali.

9. Yarda da cewa rayuwar lahira ita ce haƙiƙar rayuwa

Duniya ba gidan zama ba ce, hanya ce kawai da mutum zai bi zuwa gidansa na rayuwa, wacce ba ta da ƙarshe, ko cikin daɗi ko wuya. Wanda duk wannan aƙida ta tabbata a cikin zuciyarsa, to haƙiƙa rayuwarsa ta duniya za ta zama mai sauƙin gaske, shike nan sai ya yi ta tanadin samun tsira ranar lahira a nan duniya, kuma sai ya zauna lafiya cikin kwanciyar hankali.

Ga wani labari mai ban sha’awa na Al-Hafiz bn Hajar (Radiyallahu Anhu) a lokacin da ya ke alƙalin Misra. Wata rana ya fito cikin kwarjini da ado, sai wani Bayahude cikin tsummokara da jigata ya tsayar da shi, ya ce, “Ranka ya daɗe, tambaya nake”. Sai ya ce, “Bismillah”. Sai ya ce, “An ce Annabinku ya ce, “Duniya kurkukun mumini ce, kuma aljannar kafiri ce”, to yaya aka yi ni nake cikin wannan hali na tsiya, kai kuma ga ka cikin daula?

Sannan Hafiz ya ce: “I, duk da wannan ni’ima da na ke a ciki, in an kwatanta da ni’imar aljanna, sai ka ga kamar a kurkuku nake.

Kai kuma duk da wahalar da kake fama da ita yanzu, in an auna da azabar da za ka gamu da ita a lahira, sai ka ga yanzu kai a aijanna kake”. Sai ya ce, “Haka ne”? Sai ya ce, “Ƙwarai kuwa”. Nan take sai Bayahuden nan ya musulunta!

Saboda haka, ɗan uwa duk halin da kake ciki, ka da ka mance da lahira, domin ta fi duniya nesa ba kusa ba a ɓangaren daɗi ko wuya.

10. Zama da mutanen kirki

Haƙiƙa mutanen kirki muminai, masana, masu aiki da saninsu, masu tsoron Allah, su ne suke cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. To saboda haka, idan kana so kai ma ka sami haka, sai ka yi fatali da lalatattun abokai, ka yi abota da mutanen kirki, waɗanda za su nuna maka hanyar Allah. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce:”

Misalin aboki nagari da lalataccen aboki, kamar wanda yake zaune ne da mai sayar da turare da wanda yake zaune da maƙeri. Shi dai wanda yake sai da turare, ko bai fesa maka ba, za ka shaƙi ƙamshi. Shi kuwa maƙeri ko dai ya ƙona ka, ko ka taso da ƙaurin wuta. (Buhari/Muslim). Wato dai zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.

11. Yin afuwa da kyautatawa wanda ya ɓata maka

Tsakanin harshe da haƙori ma akan saɓa, ballantana tsakanin mutum da mutum, kuma Duk wanda ya ce: “Zo mu zauna, ya ce zo mu ɓata. Waɗannan kalmomi ne na hikima, masu ɗauke da darussa na rayuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali. To maganin saɓawa haƙuri da yin afuwa, saboda tilas sai ka ga yadda ba ka so, in kuwa ka ce duk abin da aka yi maka sai ka rama, to lallai wata rana za ka rame. Yin afuwa yana janyo wa mutum mutumci kwarjini, farin jini lada da farin ciki da kwanciyar hankali. Ga waɗansu ‘yan misalai:

Waɗansu miyagun malamai sun taɓa haɗe wa Shaihul Islam Ibn Taimiyya kai, suka yi ta cutar sa, har suka yi masa sharri, aka jefa shi a kurkuku.

Lokacin da aka sake shi, sai aka tambaye shi, ko kana tunanin ɗaukar fansa? Sai ya ce, “A’a, duk na yafe musu, ba komai, Allah ya saka musu da alhairi, wannan zaman kurkuku ya sa na yi nazarin Kur’ani na fahimci waɗansu abubuwa da dama, kuma ai su ne sanadi, na yi musu afuwa, ba wani abu”.

Wani bawan Allah ya sami labarin cewa, wani mutum ya yi da shi, ya ci zarafinsa. Sai ya ɗauki goma ta arziki, ya tafi da kansa ya kai masa har gida. Sai mutumin ya tambaye shi dalilin wannan alhairi. Sannan ya ce, “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi muku alhairi ku saka masa.” To kai ka ba ni kyautar ladan ayyukanka, ni kuma ba ni da wani abu da zan saka maka da shi, sai ɗan wannan abin duniyar. Allahu Akbar. Ɗan uwa ka ɗauki ɗabi’ar afuwa ga iyalanka, maƙotanka, da sauran al’umma, ka ga yadda za ka zauna lafiya, ka samu nutsuwa.

12. Daddaɗar Magana

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya faɗi alhairi ko ya yi shiru”.
Duk mutumin da yake aiki da wannan hadisi, haƙiƙa zai zauna lafiya da kowä, kuma zai samu kwanciyar hankali. Duk abin da zai fito daga bakinka ya kasance alhairi ne, magana ce ta gaskiya mai daɗi wacce ba za ta ɓatawa kowa ba.

13. Addu’a

Komai ya yi zafi maganin sa Allah. Kuma addu’a makamin mumini ce. Saboda haka bayan bin waɗannan mataki da sauran su, sai ka kasance kullum cikin roƙon Allah ya ba ka zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musamman ka riƙi addu’o’in zaman lafiya na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kamar wannan addu’ar.

Allahumma aslih lii diini allazi huwa ismatu amri, wa aslih Ii dunyaa ya allati fiiha ma aashi wa aslih lii aakhirati allati fihaa ma aadii, waj alil hayaata ziyaada talli fii kulli hairin waj alil mauta raahatalli min kulli sharrin.

Allahuma rahmataka arju fa laa takilni ila nafsi tarfata ainin wa aslih lii sha’ani kullihi laa ilaaha illa anta.

Allahuma inni a ‘uzu bika mnial hammi wal hazani wa minal jubni, wal bukhli, wa min galabatid daini wa ƙahnimijaali.

Waɗannan kaɗan ke nan daga abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. A dunƙule za mu iya cewa bin Allah da Manzonsa sau da ƙafa da tsarkake zuciya da jiki da mazauni da baiwa ƙwaƙwalwa lafiyayyen abincin imani da kyakkyawar niyya, su ne kaɗai za su kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Allah ya sa mu da ce. Amin.

Bayan waɗannan ƙa’i’do’ji, malamai musamman masana halin ɗan Adam, suna bayyana waɗansu ladabai ko dabaru domin zaman lafiya da mutane iri-iri. Ko da yake waɗannan ƙa’idoji da suka gabata, sun isa ga duk mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali ya rayu da su, amma duk da haka akwai waɗansu abubuwa da masana suka yi bayani, Ina ganin ya kamata a kammala wannan littafi da su.

Domin karanta cikakken bayani a kan Dabarun Zaman Lafiya Da Mutane danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Mutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

Wanna nan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceMene Ne Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?
Labarin na GabaMa’anar Tsangaya