Ma’anar Tsangaya

0
513

Kalmar tsangaya na nufin keɓantaccen wuri inda makaranta Alƙur’ani ke tattaruwa a matsayin muhalli, kuma cibiya don tsantsar koyo da koyar da Alƙur’ani Mai Girma.

Asalin kalmar tsangaya daga Barbanci ce ne(Sangaya), wadda ke nufin “masu jiran tsammani”. Akwai bambanci tsakanin makarantun allo (Moranji) da tsangaya. Makarantun Allo su ne a mafi yawan lokuta ake samu cikin birane ko garuruwa; a inda iyaye ke kai ‘ya’yansu maza da mata don koyon karatun Alƙur’ani Mai Girma. ‘Yan makarantar allo kan zo makaranta da safe, sannan su koma gida bayan an tashi, sai kuma da yamma a dawo.

Babban bambamcin tsangaya da Makarantar Allo shi ne, almajiran tsangaya suna rayuwa dindindin a cikin makaranta, ƙarƙashin kulawar alaramma. Ɗaliban tsangaya su ne almajirai, kuma a mafi yawan lokaci, tsangaya na ƙunsar tsansar maza ne ba mata ba.

Kodayake akan samu ‘yan ƙananan yara mata da ke zama kusa da alaramma a matsayin ‘yan makarantar allo cikin tsarin tsangayaa.

Hausawa kan kira Makarantar Allo da suna “Makarantar Toka”, waɗansu lokuta kuma akan ce makarantar Muhammadiyya.

Alaƙar ƙabilun Arewacin Najeriya da Alƙur’ani alaƙa ce mai zurfi. Da yawa akan samu ƙabila Musulma na da kishin karatun Alƙur’ani Mai Girma; musamman ma idan sun daɗe da karɓar Musulunci. Sai dai irin ƙaunar da ƙabilun Kanuri da Hausawa da Fulani ke nunawa ga Alƙur’ani ta kere sauran.

Yawaitar tsangayu da adadi na dattijan malamai da samari cikin biranen da waɗannan ƙabilu ke rayuwa; wata hujja ce ga fifikon da ke akwai.

Domin karanta cikakken bayani a kan Zubin Tsangaya danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Misalan Waƙafi Ababen Koyi A Tarihin Musulunci danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAbubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali
Labarin na GabaYadda Zubin Tsangaya Yake