Mene Ne Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?

0
304

Zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne burin dukkan ɗan Adam maza da mata; manya da yara musulmi da kafiri babu wani saɓani.

Za mu iya cewa, yanayin nutsuwa da jin daɗi da farin ciki, annashuwa da samun gamsuwa a zuci Ga kuma waje; ba tare da wani tsoro ko fargaba ko damuwa ba, a kan abin da ya wuce, ko tsoron abin da zai zo; waɗannan abubuwa in sun haɗu, ana iya kiran su zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wannan an ɗan kusanto da ma’ana ce kawai, amma a gaskiya sanin haƙiƙanin zaman lafiya da kwanciyar hankali sai wanda yake cikinsa. Larabawa suna kiran sa “Sa’adah” kuma suna fassara shi da cewa kishiyar wato tsiya.

Rukunan zaman lafiya da kwanciyar hankali guda uku ne:

1. Ingantacciyar zuciya da jiki.
2. ingantacciyar rayuwa.
3. Kyakkyawar makoma.

Duk mutumin da zuciyarsa ta gurɓata da kafirci da bidi’a da zalunci da sha’awa da sauran su, ko jikinsa ya yarda da lalaci da son hutu kowane lokaci da karɓa ba bayarwa, haƙiƙa wannan mutum ba shi ba zaman lafiya, ballantana kwanciyar hankali.

Haka kuma duk mutumin da ya ɗaukar wa rayuwa ta ƙarya, mara tabbas, mai cike da ruɗani da hauma-hauma, wacce ba ta da wani tushe ballantana makama, shi ma ba zai shiga cikin masu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

Sanin kyakkyawar makoma da tabbacin inda aka dosa yana da muhimmanci wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Yanzu a haɗa musulmi da ya yarda da Allah da ranar Lahira da wuta da aljanna, da kafiri wanda shi kawai duniya ita ce farko ita ce ƙarshe a wurinsa?

To amma wacce hanya ce mafificiya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali? To mai karatu sai in ce maka nan fa ake yin ta; saboda duk mutumin da ka yiwa wannan tambaya, zai ba ka amsa saɓanin ta ɗan’uwansa. Mutane da yawa suna cikin ruɗani game da wannan amsa; kowa kuma aiki yake yi tuƙuru domin tabbatar da ita a kan kansa.

Amma fa kashi casa’in bisa ɗari sun yi hannun riga da hanyar ba da amsa ingantacciya. Kafin na ba da amsa, bari mu yi nazarin kaɗan daga cikin ruɗu da mutane da dama suke ciki, game da hanyoyın samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceHikimomi A Kan Wadatar Zuci
Labarin na GabaAbubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali