Tag: ilimin lafiya

  • Yadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake

    Yadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake

    Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi, kamar haka;

    • Ƙurajen gaba
    • Ƙaiƙayin gaba
    • Fitar da farin ruwa mai kauri
    • Jin zafi idan za a sadu
    • Jin zafi idan za a yi fitsari
    • Ɗaukewar sha’awa
    • Kunburin mara ko ciwon mara
    • Ƙanƙancewar azzakari ga namiji
    Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi. Duk da yake fitar da farin ruwa a gaba yana daga cikin babbar alamar ciwon sanyi, amma shi kansa farin ruwa ba kowanne yake da matsala ba. Akwai mara matsala. Shi kansa farin ruwan da yake fita ya kai kala huɗu, ga su kamar haka;
    • Akwai mai fita fari tas, kamar koko mai kauri mara yauƙi ko kamar madara;
    • Akwai mai fita kamar gasara ko kuma in ce kamar kitse, wata ma sai ta sa hannu a ciki tana zaro shi;
    • Kuma akwai mai fitowa kamar zare a rinƙa zaro shi kamar zare, da ya taɓa jiki sai ya bushe;
    • Sannan akwai mai fita kamar majina mai haske mai ƙyalli mai yauƙi.
    Duk a cikinsu guda uku na ciwo ne wanda ba a sonsu a jikin mace. Wanda ake so shi ne mai fitar kamar majina, mai yauƙi, wannan shi ne ruwan ni’ima. Idan mace ta rasa shi a jikinta to akwai matsala. Samuwar ɗaya daga cikin ukun nan a jikin mace yakan hana wannan zuwa, daga nan sai ka ga mace ta shiga cikin damuwa. Domin karanta cikakken bayani akan Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi danna nan Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Hanyar Korar Aljanu Da Kariya Daga Dawowar Su

    Hanyar Korar Aljanu Da Kariya Daga Dawowar Su

    Kamar yadda muka sani aljani wata halitta ce da Allah ya yi ta ya kuma ɓoye ta ba za mu ganta ba; amma ita Allah ya hore mata za ta ganmu. Kamar yadda Allah (Subhanahu Wata’ala) ya faɗa a cikin Alƙur’ani mai girma a suratul A’araf aya ta ashirin da takwas (28).

    Sannan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace aljanu sukan shiga jikinmu kamar yadda jini ke gudana a cikin jikinmu; da haka muke sanin cewa aljanu suna ma da haƙuri dan sun fi mu haƙuri. Don da mu ke ganinsu, su ba sa ganinmu, kuma mu shiga cikin jikinsu kamar yadda Allah ya hore musu su shiga cikin namu, da mun cutar da su fiye da yadda suke cutar da mu. Da haka ne za ka gane lallai aljanu suna da haƙuri fiye da mu mutane. Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Nau’ikan Aljanu Suke danna koren rubutun nan. Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Za A Gane Matsalolin Aljanu Tare Da Magance Su danna koren rubutun nan. Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu
  • Yadda ake Yiwa Jarirai Hudubar Haihuwa

    Yadda ake Yiwa Jarirai Hudubar Haihuwa

    Akwai hanyoyin biyu da za a iya yiwa jarirai huduba wanda suka tabbata a suna bisa tsarin addinin musulunci kamar haka:

    Hanya ta farko.

    Yana daga cikin abin da yatabbata a sunna idan aka haifi jariri sai mahaifinsa ko wani wanda mahaifin sa ya wakilta,ya dauki jaririn ya kara bakin sa adaidai kunnen sa na dama,ya kira sallah, yadda ake kiran sallah da kalmomi guda (19) kamar haka:

    Idan da maimaici kenan,ko guda (17) idan babu maimaici kenan,ga misali na guda (19)

    “Allahu Akbar Allahu Akbar, Allahu Akbar Allahu Akbar,

    Ashhadu an Laa iLaaha illal Laah, ashhadu an Laa iLaaha illal Laah

    Ashhadu anna muhammudur rasulul Laah ashhadu anna muhammadan rasulul Laah,

    Hayya alal Salah hayya alal Salah

    Hayya alal falah, Hayya alal falah

    Allahu Akbar Allahu Akbar,

    Laa iLaaha illal Laah.”

    Sannan ya kara bakin sa a daidai kunnen sa na hagu,nanma sai ya tayar da iqama kamar haka

    “Allahu Akbar Allahu Akbar

    Ashhadu an Laa iLaaha illal Laah,

    Ashhadu anna muhammadan rasulul Laah

    Hayya alal salaati, Hayya alal Salah,

    Qad qaamatus salaatu, qad qaamatus salah,

    Allahu Akbar Allahu Akbar

    Laa iLaaha illal Laah.”

    Sannan sai yace sunan ka wane,kamar misali sunan ka/ki (Ahamad ko Zainab).
    Toh kuma daga nan Idan mahaifin yana so sai yayiwa yaron (tahaniki) abin nufi da (tahaniki)shine kasa dabino a bakin ka idan ka gatsa shi sai a sakawa jariri a bakin sa kafin a bashi wani abinci, amma ba hakan yana nufin uwa baza tabashi ruwan nono mai kauri kalar rawaya da ake kira daKushi da harshen hausa ba.

    Zata bashi idan jariri na bukata sannan sai a bashi dabinon da aka gatsa ya tsotsi ruwan wannan shima yana cikin abinda akewa jariri da zaran an haife shi.

    Hanya ta biyu:

    Za ayiwa jariri (tahaniki) idan mahaifin sa naso sannan yace sunan wane, misali yacewa jaririn sunan ko sunan ki(Ahamad ko Zainab) ba tare da yin kiran sallah a kunnen dama da tayar da iqama a kunnen hagu ba.

    Domin karanta yadda zakai tarbiyar yaro danna nan 

  • Ciwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure)

    Ciwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure)

    Wasu suna sakata daya daga cikin psychiatric disoders domin ciwone dayake shafar ƙwaƙwalwa 

    Ciwon farfadiya cuwo ne wandda yake zuwa da yawan jijjiga sakamakon excesive electrical discharge daga kwakwalwa yawancin jijjigar takan faru tsakanin sakanni 30 zuwa mintina 2.

    yayinda mai fama da wannan ciwo ya taso masa yana buƙatar abasa agajin gaggawa

    Yadda za’a taimakawa mai wannan ciwon wanda zai bada agaji ya nutsu sannan yatabbatarwa da mutane zai iya bayar da agajin

    A cire duk wani abu wanda yakan iya matsewa mara lafiya wuya ya tare mishi numfashi irinsu maballin riga na wuya,neck tie ko sarqar wuya,velt da sauransu 

    Kada a riƙe mara lafiyar da niyyar tsayar da jijjigar,hakan ka iya haifar da babbar matsala

    Kada a saka komai a bakin mara lafiyar,ko ayi ƙoƙarin riƙe mishi harshe ko kuma bude bakinshi,idan hakan bazai yuwuba a samu dai a dafe masa baki domin taimakawa karya daddatsa harshensa 

    A saka wani abu mara tudu sosai kuma mai taushi a kasan kansa domin gujewa fasa kai saboda jijjigar dayakeyi 

    Bayan jijjigar ta tsaya a ƙwantar da mara lafiyar a barin jikinshi na dama ko na hagu

    saboda ya samu sararin yin numfashi.

    Kada a rabu da mara lafiyar bayan jijjigar ta tsaya har saiya dawo cikin hankalinsa domin rashin hakan zai iya sakashi cikin dimuwa

    Domin karanta maganin Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction) Dan nan ko kuma bayani akan lalura shanyewar barin jiki shiga nan

  • Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction)

    Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction)

    Ma’aurata kunsan ciwon sanyi da rashin  tsafta suna matukar sa rashin sha’awan jima’i kuwa? Suna hana jituwa tsakanin mata da miji. Kuma komi iya kwanciyarki da cushecushen kayan mata inbaki magance infection ba akwai matsala. 

    Irin wannan infection din yana hana jin dadin jima’i,yana hana daukar ciki,yana kuma cutar da maigida ya cutar da abokiyar zama ma inba ke kadai bace.

    Domin akan sami amarya me tsafta, yayin da uwargida kuma ƙazama, ko kuma uwargida me tsafta yayin da amarya kuma me ƙarancin tsafta… wanda illar infection shine idan mijin zaijewa waccan me ƙarancin tsaftar kuma kema yazo miki toh duk ƙoƙarinki tsaftarki bazaki tsira ba sai dai abun yai miki da sauki.

    Alamomin Sun Hada Da
    • Ɗaurewar mara akai akai ba lokacin period ba
    • Jin motsi kamar wani abu na tafiya acikin farji
    • Jin zafi yayin fitsari
    • Jin zafi yayin saduwa
    • Ganin fitar farin ruwa me kauri
    • Ganin fitar abu kamar dusa-dusa daga farji
    • Jin discharge na fita da karni kamar karnin kifi ko ɗoyi
    • Kai kayin gaba
    • Gani kurji ko kumburi a gaba.

    Al’amarine me nauyi amma kar ai kunyar zuwa ga likita neman lfy,wasu na dashi amma sam basusan menene ba sai daga baya in abun yayi yawa,wasu kuma basa ganin discharge din komi saide ciwon mara…. shima maganin dinsa daban. shi yasa ko yaushe nake cewa aje  ƙwararrun jami’an lfy.

    Ga jami’an lafiya musamman ƙananu kusani vaginal infection ya kasu iri da yawa akwai viral,bacterial,fungus da parasitic don haka wajibi ne ka fahimci meke jawosa kafin dora mutum a magani,ba duk infection ne ake bada antibiotics ba,akwai infections din da inka ba mace antibiotics ka kara haukatashi ne.

    Sannan kuskure ne dora mutum akan babban antibiotics wato broad spectrum antibiotics akan ƙaramin abunda bai kai ya kawo ba,hakan kuma kan jawowa jikinsu yai developing antibiotics resistant ta yadda zaima ki aiki nan gaba in wata cutar ta samesu,a kiyaye narrow spectrum sune first line ko yaushe na antibiotics. 

    Don haka wajibinku ne ku fahimci abunda ya jawo infection din da kyau kafin bada magani,shi yasa manyan asibitoci wasu sai mun dau sample na discharge din mun turawa masanan kimiyya wato medical lab scientists sun tantance mana domin dora mutum kan maganin da ya dace dashi.

    Sannan yana da kyau jami’in lafiya yasan waɗanne irin tambayoyi ya dace yai da kuma sanin dalilin yin su,karkurum mace tazo da complain, kai kuma ka saki layi ka tafi wata tambayar can mara mahimmanci  da  bata da alaqa da matsalarta… daga lokacin bazata kuma dawowa gurinka ba domin zata fahimci kaima din bakasan komi ba. 

    Sannan ku dai na jin haushi don an muku tambaya kusani ayanzu ƴancin mara lafiyar da yazo gabanka ne.. ya tambayeka daya bayan daya game da maganin daka rubutamasa, kai masa bayani kuma har sai ya gamsu, sannan yana da hakkin ka sanar dashi damuwarsa matuƙar akwai buƙatar hakan domin yasan abunda zai kiyaye…. Don haka batun wani harden rubutu a likitanci yanzu bashi. Kai rubutun magani straight and clear shine sanin aiki.

    Don haka jami’in lfy a duk sanda mace ta zoma da korafi na alamun infection ne ke damunta baya ga magani karku mance da bata wadannan shawarwarin da zan lissafo; sune ginshikin cin nasara wajen magancesa. Ku sanar da ita cewa;

    1. Zaifi kyau ki riƙa sanya pant na cotton bana roba ba. Sannan a rika canza pant din sau 2, 3 zuwa 4 a rana a irin wannan yanayin. Dalilin shine farji ba gurine da iska ke ratsawa ba ko yaushe sanya panta na roba karawa gurin danshi zaiyi… danshi ko yanayi ne da irin wadannan kwayoyin cutar keso. 

    2. Duk sanda zaki wanke unders dinki kike amfani da ruwan dumi kina wankewa dashi, inkuma ruwan na sanyine to a zuba gishiri aruwan wankin kadan domin kashe wasu ƙwayoyin cutar koda akwaisu ajiki. Sannan idan da  hali ake shanyasu acikin daki ko ida akasan ƙurar ƙasa bazatake tasowa tana badesu ba kafin su bushe.

    3. Sannan akiyaye kai hannu wajan farji,  yana dakyau hannu ya zamto anwankeshi kafin a shiga bayan gida koda babu datti da kuma bayan anfito.

    4. Kar kike tura sabulu yayin wanke farji zuwa ciki, inda hali ma sam babu buƙatar sabulu wajen wankesa domin gurine dake wanke kansa da kansa, shyasa wani lokacin kina zaune kurum sai kiga abu me yauki na fita. 

    Sannan ake aske gaban fes duk bayan sati 4 ko 6. Amma akeyi sama-sama, sannan ba direct ba, ko yaushe kafin ki askin ki sami ruwan duminki ki zuba a roba kikai bandaki inkinje ki zauna aciki na minti 5 zuw 10 tukun kafin fara shaving din saboda yin hakan zai hana kuraje da kaikayi…. bama sai me infection ba ga dukkan maza da mata ya dace kuyi hakan. Idan da hali a sa gishiri cikin ruwan dumin kafin azauna ciki.

    5. A tabbatar da tsafta bandakuna pls, Ake kaɗa ruwa da gishiri ko da Omo ana watsawa acikin bandakin ana wankesa, ko ta hanyar amfani da sauran maganin kashe kwayoyin cuta na ruwa.

    6. Ake tsarki da ruwan dumi zaki iya dumamawa ki zuba a cikin flask duk sanda zaki kama ruwa sai ki tsiyaya in kina gida. sannan anaso ake sa gishiri daidai misali a ruwan dumin da za’ake tsarkin. A daina tsarki da ruwan sanyi sam idan da hali amma inba yadda Za’ai to shima asa gishiri kadan ciki. Ko namiji inda hali inkana gida ka jimanci tsarki da ruwan dumi.

    7. kike canza fant yayin period akalla Sau 3, xuwa 4 a rana, insun Jima koda basu ɓaci da jini ba. Saboda jinin al’ada. ne me kyau dake ba ƙwayoyin cuta damar rayuwa…

    8. Matsayinki name fama da infection Idan da hali inke kadai ke kwanciya adakinki ki rika cire pant dinki inzaki kwanta ki bar iya siket yadda iska zatake ratsawa zuwa wayewar gari ki rika haka kullum har matsalar ta tafi.

    9. Karka mance duk matar auren da tazo da Infection wajibi ne mijinta ma adorasa a magani daidai da irin nata, hakama insu 2 ko 4 ne wajen mijin kaf dinsu sai sunsha maganin daidai da nata.

    Inde an kiyaye wannan Insha Allah za’a samu sassauci akan kari, magani kadai babu counseling a infection baya aiki… abun dadin ma yawancin magungunan infection ma wani sha sau 1 ne shikenan wani kuma sau 2 anjima anayi kwana 5 saide in ansami treatment failure. Fatan harma wadanda basu dashi sun ilmantu.

    Domin karanta bayani akan sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i Danna nan

  • Sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i

    Sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i

    Wannan kalan ciwon sanyin ana kamuwa da shi ne ta hanyar jima’i wato. Mata zata iya shafawa mijinta idan tana mu’amala da wasu mazan.  Haka shima zai iya shafawa matar sa idan yana da mata sama da ɗaya ko kuma idan yana neman mata.

    Namiji ba kasaifai yake ganewa yana da wanann cutar ba saboda alamominta basu cika bayanna a jikin namiji ba. Yawanci sai idan ciwon ya bayyana ajikin mace, wajen neman maganin sai ya gane shima yana dashi.

    Amma Idan Anyi Sa’a Ya bayannana Cikin Namiji Akwai Alamomin Kamar Haka;

    1. Jin zafi wajen fitsari
    2. Jin zafi bayan fitan maniyyi
    3. Fitar farin ruwa kaɗan
    4. Ƙaiƙayin gaba
    Alamomin a Jikin Mata
    1. Ƙaiƙayin gaba
    2. Jin zafi wajen fitsari
    3. Warin gaba
    4. Fitan ruwa mai launin yellow ko kore ko fari tass.
    5. Kwailewar farji

    Amma akwai wasu ɗabi’un da mata keyi hakan na jawo shi wannan ciwo na sanyi wato (infection)

    1. Yanayin tsaftace farji:

    Wasu matan na amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu,  a ganinsu hakan shi ne dai dai. Kaninfari da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami,medicated soaps da sauransu.

    Wanann ba tsaftaceki za suyi ba, hasalima kina ƙara ɓata halittar farjinki. Kaman yadda mukayi bayani a baya ga me da normal flora, yawan amfani da abubuwannan na kashe wannan hallitun na normal flora a cikin farjinki. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitarsa, saboda haka er uwa ki dinga amfani da ruwan dumi kawai wajen tsaftace kanki.

    1. Yanayin wanke dubura bayan:

    kinyi bayan gida: Asalin yadda ya dace ki wanke bayan gida shi ne ki fara daga gaba zuwa baya, ma’ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka suke yi. Wannan ɗabi’ar sam bata da ce ba. Idan kika fara daga baya kina ɗebo ƙwayoyin cutar da ke cikin bayan gidanki kina aikawa cikin farjinki. Hakan zai janyo miki da matsala babba. Shi farji baya san baƙon abu a tattare dashi.

    Domin karanta Larurar Sanyin Gaba Wato Genital Infaction  Ko Ciwon Hanta  danna koren rubutun nan

  • Matakin Kariya Kafin Samun Ciki (Preconceptional care)

    Matakin Kariya Kafin Samun Ciki (Preconceptional care)

    Wannan wasu matakan kariya ne da mace da ta ke da shirin ɗaukar ciki ya kamata ta samu tun kafin samun cikin, domin samun cikarkiyar lafiya lokacin rainon ciki da kuma haihuwa.

    MENE YA SA KIKE BUƘATAR MATAKAN KARIYA KAFIN SAMUN CIKI?

    Tabbatacciyar lafiyar mace kafin samun ciki, yana ɗaya daga cikin manyan mahangar samun lafiyayyen ciki da haihuwa.

    MATAKAN KARIYA.

    1. Ga macen da ta ke da wata cuta da ta ke shan magani a kai, ya kamata likita ya tabbatar mata da cewar cutar ba ta matakin da za ta iya ba ta matsala idan ta samu ciki, wannan cututtuka sun haɗa da:
      -ciwon siga
      -Sikila
      -Asma
      -Ciwon zuciya
      -Hawan jini…… Da sauran su.
      Baya ga haka, akwai wasu maganin da ake sha a waɗannan cututtuka, wanda ka iya ba wa jaririn da za ta haifa matsala, don haka, likita zai canza mata su zuwa ga wanda ba su da matsala a kan jariri.
    2. Folic Acid
      Wannan magani mace kan fara shan sa kafin samun ciki da kuma wata 3 na farkon ciki, bisa shawarar likita. Yana bayar da kariya a kan haihuwar yara masu ƙaramin kai ko buɗaɗɗiyar laka.
    3. Abinci.
      Akwai buƙatar mace ta ƙara samun abincin mai gina ciki da ƙarin lafiya domin ita kanta da kuma jaririn da zai zauna a cikinta.
    4. Barin shan magani barkatai ba tare da shawarar likita ba, saboda akwai magungunan da suke bayar da matsala ga jariri ko su kawo ɓarewar cikin, idan aka samu.

    Danna koren rubutun nan domin karanta Alamomin Shigar Ciki (Juna Biyu) ko yadda ake amfani da na’urar gwajin ciki ko Yadda za ki kare kanki daga Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

  • Ciwon Sanyi (TOILETS INFECTION)

    Ciwon Sanyi (TOILETS INFECTION)

    Ciwon Sanyi wato (Toilets Infection) mutane kan kira wasu cututtuka da suna Toilet Infection a al’adance, a sani cewa, babu Wani ciwo da toilets ya ke haddasawa ko kawowa, abin da kawai aka sani shi ne akwai miliyoyi na micro organism waɗanda sukan rayu cikin toilets kamar na cikin ruwa, iska, ƙasa da jini, waɗannan ƙwayoyin halitta su ne kan haddasa cutuka da dama, waɗanda akan ɗauka daga wani zuwa wani ta hanyar toilets ɗin.

    Abin dai ba ya rasa nasaba da cinkoson jama’a a banɗaki ɗaya, kamar makaranta, gidan hanya, da kuma rashin tsafta, su ne kan kai ga ire-iren waɗannan cututtuka da ake wa suna toilets infection bisa kuskure.

    Wajibi ne mu tsaftace muhallinmu musamman toilets, mu yi amfani da antiseptic duk lokacin da mu kai amfani da toilets ɗinmu, mu riƙa koya wa yaranmu amfani da sabulu ko toka duk lokacin da suka fito toilets, tare da rufe toilets ɗinmu a ko yaushe, wannan yakan rage kamuwa da cututtuka da dama waɗanda za a iya ɗauka ta hanyar toilets.

    Domin karanta yadda ake gyara soyayya ko Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki ko yadda ake wa maigida lokacin al’ada ko Amfani Da Kuma Illar Magungunan Ƙara Ƙarfin Maza (MALE SEX ENHANCEMENT SUPPLEMENTS)

  • Amfani Da Kuma Illar Magungunan Ƙara Ƙarfin Maza (MALE SEX ENHANCEMENT SUPPLEMENTS)

    Amfani Da Kuma Illar Magungunan Ƙara Ƙarfin Maza (MALE SEX ENHANCEMENT SUPPLEMENTS)

    Tabbas saduwar aure a tsakanin namiji da mace tana da matuƙar muhimmanci a zamantakewar aure. Duk da kasancewar ba ita kaɗai ba ce ta ke samar da morewar zaman aure. Saduwa ita ce a kan gaba.

    Wannan yana nufin cewa ko da mace tana da ladabi da biyayya, iya magana, iya girki, iya kwarkwasa, iya kwalliya, tsabta da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkan su ba su kai muhimmancin saduwa ba a wurin mijinta.

    Haka nan kuma, ko da namiji yana da ƙoƙarin samar wa matarsa da abinci da abin sha, sutura, wurin zama, kiwon lafiya, tsare mutunci, tausayawa, kyautatawa da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkansu ba su kai muhimmancin saduwa ba a wurin matarsa. Bisa wannan dalilin ne maza su ke jajircewa wajen ganin cewa sun gamsar da matansu ta fuskar jima’i.

    ABIN DA AKE NUFI DA GAMSAR DA JUNA WAJEN SADUWAR AURE (SEXUAL SATISFACTION)

    Masana a fannin lafiya (medical health), da na addinin Musulunci (Islamic clerics), da na halayyar ɗan-adam (psychologists) sun kai sun komo ga me da ma’anar gamsar da juna a wurin saduwar aure. Amma duk bayanansu sun tattara ne a kan cewa ma’anarsa ita ce, “A samu natsuwar da za ta gusar da duk wata sha’awa bayan an gama saduwar, sai kuma wani lokaci idan buƙatar hakan ta taso”.

    Da wannan ne wasu da yawa daga cikin mazajenmu su ke ɗaukar cewa mutum ba zai iya gamsar da iyalinsa ba sai:

    1. Idan yana da al’aura mai kauri, ko tsawo, ko kuma duka biyun.
    2. Idan yana daɗewa wajen saduwa.

    Hakan ne ya bai wa wasu kamfanoni masu sarrafa magungunan Bature, da kuma masu maganin gargajiya damar samar da magunguna iri-iri waɗanda aka ce suna bai wa namiji ƙarfin gamsar da iyalinsa yadda ya kamata. Abin ya yi yawa sosai, ta yadda masu waɗannan magunguna suka cika chemists, da kasuwanni, tituna, da tashoshin mota suna cin karensu babu babbaka.

    RABE-RABEN MAGUNGUNAN BATURE NA ƘARA KARFIN NAMIJI

    Magungunan sun kasu kamar haka:

    1. Kwayoyi (drugs): waɗannan su ne magungunan da ake sha da baki, kuma suna da yawa. Sun haɗa da Viagra, VigRX Nitric Oxide , TestRX, GenF20 Plus, Semenax, ProSolution Plus, VigRX Plus, Extenze, da sauransu.
    2. Mayuka (creams): waɗannan su ne magungunan da ake shafawa. Su ma suna da yawa, kamar Maxman Delay Sex Cream, Viamax Maximum Gel, TITAN Gel, Doc Johnson Power Plus Delay Cream, Man1 Oil Penile Health Cream, Lavenda Massage Oil, da sauransu.
    3. Allura (injection): waɗannan su ne magungunan da ake yin allura da su. Su ma suna da yawa, kamar Papaverine, Prostaglandin E1 (PGE1), Phentolamine, Alprostadil, Trimix, da sauransu.
    4. Tiyata (surgery): wannan ita ce aikin yanka mazakuta da ake yi a ɗakin tiyata domin a ƙara mata tsawo ko kauri (penile augmentation surgery) ta hanyar sanya wata roba mai kama da jijiyoyin mazakuta (medical grade silicone). An fi yinta a ƙasashen Turawa, kuma tana da tsada sosai.
    5. Jiƙe-jiƙen magungunan gargajiya (herbal concoctions): wannan shi ne ya fi yawa a cikin al’umarmu. Su ma akwai na sha akwai kuma na shafawa. Masu ilmin kimiyya ba su cika yarda da tsabtar waɗannan magungunan ba, haka kuma ba su yarda da sahihancin ƙa’idar amfani da su ba (dosage).

    TASIRIN MAGUNGUNAN ƘARA ƘARFIN NAMIJI

    Masu amfani da waɗannan magunguna suna ganin tasirinsu. Hakan ba ya rasa nasaba da abubuwan da ake haɗa su da shi, kamar ginkgo biloba, ginseng, DHEA, horny goat weed, fenugreek, maca da sauransu. Wasu chemicals ne wasu kuma ana tatso su ne daga tsirrai, sa’annan suna sanya ƙaruwar zubar sinadarai (hormones) a cikin jiki ne. Amma a gaskiya sakamakon binciken kimiyya da yawa ya tabbatar da cewa daɗewa ana amfani da su yana haifar da illa ga lafiyar mutum. Bayan wannan kuma, idan jikin mutum ya saba da su, to, zai yi wahala ya iya saduwa da matarsa in bai yi amfani da su ba. Assha! Ka ga kenan matsala ta auku.

    SIRRIN GAMSAR DA MACE WAJEN SADUWAR AURE

    Alqur’ani mai girma ya gama mana komai, domin ya sanar da mu yadda za a gamsar da mata wurin saduwa:

    نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا لِأَنْفُسِكُمْ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ مُلَاقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ

    “Matanku gonakinku ne, ku shiga gonakinku ta yadda ku ke buƙata, kuma ku yi wasanni da su (a lokacin da za ku sadu da su)”, Baqarah: 223.

    Kenan idan mutum ya yi wasanin motsa sha’awa sosai kafin ya fara saduwa da iyalinsa, to, insha-Allahu zai gamsar da ita. Wasu suna yin kuskuren fahimtar cewa daɗewa ana saduwa shi ne kwazo da burgewa. A likitance wannan ba gaskiya ba ne, domin ana so ne saduwa ta zama daga minti 3 zuwa 17. Idan ta kai minti 20, to, ta yi yawa domin za ta iya sanya ni’imar matar ta ɗauke, daga nan sai ta fara jin zafi, ƙila ma a yi mata rauni. Amma a lura ba wai ina nufin dole kada a wuce abinda na faɗa ba ne, domin wani yana iya yin minti 60 ma ba tare da matar ta tsawwala ba.

    MENE NE ABIN YI?

    1. Matsalar ƙanƙancewar gaba gaskiya ce. Idan mutum yana da ita, to, ya kamata ya tuntuɓi likita, domin a ɗora shi a kan maganin da ya dace, maimakon saye da kuma amfani da magunguna barkatai, waɗanda idan illarsu ta taso, bai san yadda zai magance ta ba.
    2. Idan ba ya zama dole ba, kada ka saba ma madam da daɗewa ana saduwa, domin idan ka daina daɗewa daga baya, to, akwai matsala fa.
    3. Ka ƙarfafa wasanni kafin ka fara, kamar yadda Alƙur’ani ya yi umarni.

    WalLahu A’lam

    Domin karanta yadda ake gyara soyayya ko Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki ko yadda ake wa maigida lokacin al’ada

  • Matsalar Fata Da Ke Ɓangaren Ido (CONJUNCTIVITIS)

    Matsalar Fata Da Ke Ɓangaren Ido (CONJUNCTIVITIS)

    Matsala ce da ke faruwa ga ido, wani lokacin tana shafar ido ɗaya; wani lokaci kuwa za ta shafi idanuwan, idan har ido ɗaya ya fara, to ɗayan shi ma nan take zai harbi ɗaya.

    Wannan ciwon ƙwayar viral infection ce ke kawo shi, wani lokacin kuwa “Bacterial infection”, ya danganta da yanayin ciwon. Kuma ciwon kan bayyana a cikin kwana biyu zuwa mako uku (days-3wks).

    ALAMOMI

    Wani lokacin za a ga alamomin wannan ciwon kamar haka:
    -Ƙaiƙayin ido
    -Kumburin ido
    -Canzawar ƙwayar idanuwa
    -Zubar ruwa
    -Rashin son hasken rana, ko wani kalar haske na daban,
    -Da sauran Alamomi.

    Wannan ciwon conjunctivis a kan iya ɗaukar sa ta waɗannan hanyoyi kamar haka:
    -Amfani da hankicif wanda mai wannan ciwon ke amfani da shi wurin shafe fuskarsa.
    -Ko kuma gaisuwa idan mai wannan ciwon ya shafi idanuwansa.
    -Da amfani da wasu hanyoyi marasa tsafta.

    SHAWARA

    -Tsaftace muhalli na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar ɗan Adam
    -Hana yara zuwa makaranta idan sun kamu da wannan matsalar, domin gudun wasu su kamu
    -Amfani da maganin antimicrobial na mai ko na ɗigawa
    -Kawar da cutar ga yara musamman gonococcal_conjunctivitis
    Idan kuwa abin ya yi tsanani, to sai a yi gaggawar zuwa asibiti domin ganin likita kai tsaye.

    Domin karanta menene cutar Sikila danna koren rubutun